--
Mutuwa Rigar Kowa: Jigo a Izala, Sheikh Adam Muhammad, ya mutu

Mutuwa Rigar Kowa: Jigo a Izala, Sheikh Adam Muhammad, ya mutu



ROHOTON: https://hausa.legit.ng/news/

Ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, ya warware jita-jitar da wasu jaridun yanar gizo ke yadawa a kan cewa shugaban JIBWIS, Sheik Bala Lau, ya mutu a daren ranar Asabar. A cikin wani sako da ya wallafa a sahfinsa na 'Facebook', Pantami ya ce masu yada labarin basu samu bayaninsu daidai ba. Pantami ya ce Sheikh Bala Lau yana nan da ransa, cikin koshin lafiya. Kazalika, ya nemi jama'a su yi watsi da duk wata jita-jitar cewa ya mutu.

A cewarsa, hotunan da ake yadawa na jana'izar Shaykh Adam Muhammad Gashua ne tare da yin fatan cewa kafafen yada labarai zasu gyara kuskuren da suka yi wajen sanarwar da suka fitar. Jaridar SaharaReporters ta wallafa labarin cewa Sheik Bala Lau ya mutu ranar Asabar da daddare. Inda ta wallafa wasu hotuna da sunan na jana'izarsa ne da aka yi yau, Lahadi, 10 ga watan Mayu.

Jama'a da dama sun nuna shakku a kan labarin na SaharaReporters. Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa, ya sanar a shafinsa na tuwita cewa ya yi magana da Sheikh Lau bayan ganin labarin da SaharaReporters ta walla a kan cewa ya mutu. Har ya zuwa wanna lokaci, SaharaReporters ba ta janye labarinta ko gyara kuskuren da ta yi ba, lamarin da yasa wasu ke zargin cewa da gangan suka yada labarin domin cimma wata manufarsu.

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Mutuwa Rigar Kowa: Jigo a Izala, Sheikh Adam Muhammad, ya mutu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?