LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Anrushe wasu manyan Otal 2 da suka karya dokar kulle a Fatakwal (Hotuna}ROHOTON:https://hausa.legit.ng/news/

An rushe Otal din Prodest da ke Eleme da Otal din Etemeteh da ke Onne bayan gwamnatin. Ribas ta zargesu da karya dokar kulle Fatakwal, babban birnin jiha. Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ne ya bayar da umarni tare da jagorantar rushe Otals din a ranar Lahadi. Bayan ya saka dokar kulle Fatakwal, gwamna Wike ya bawa Otal - Otal da ke jihar umarnin su dakatar da aiyukansu domin dakile yaduwar annobar korona.

Wike ya gargadi mazauna jihar cewa za a dauki matakai masu tsauri a kan dukkan wanda aka samu ya na karya dokar kulle jihar. A ranar Lahadi ne Wike ya jagoranci rushe Otal din Prodest da ke Eleme yayin da sauran jami'an gwamnatinsa suka wuce Onne domin rushe Otal din Etemeteh. Gwamna Wike ne da kansa ke fita domin tabbatar da cewa jama'a sun yi biyayya ga dokar kulle jihar da gwamnatinsa ta saka.


A kwanakin baya ne Wike ya bayar da umarnin a killace wasu mutane a cibiyar duba masu jinyar korona. An kama mutanen ne suna yawo ba tare da wanin uzuri da gwamnati ta yarda da shi ba. Kazalika, Wike ya bayar da umarnin yin gwamjon wasu dabbobi da manyan motocin da aka kama sun shigo da su jihar Ribas.

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments