--
Ina nan da rai na - Shiekh Bala Lau Yayi Martani Mai Zafi

Ina nan da rai na - Shiekh Bala Lau Yayi Martani Mai Zafi



ROHOTON: https://www.bbc.com/hausa

Shugaban ƙungiyar Izala a Najeriya Shiekh Abdullahi Bala Lau ya ƙaryata labarin mutuwarsa da kafar yaɗa labarai ta Sahara Reporters ta wallafa a shafinta na intanet da kuma Twitter a ranar Lahadi.

Shiekh Bala Lau ya shaida wa BBC cewa "Ina nan lafiya lau."

A labarin da ta rubuta da ya tayar da hankalin ƙungiyar Jama'atul Izalatul bid'ah wa Iqamatus Sunnah, Sahara Reporters ta ce shugaban ƙungiyar ya rasu a ranar Asabar.

Ta kuma wallafa hotonan jana'iza a shafinta na Twitter tare da hoton gawar da ta ce ta Shiekh Bala Lau ce da aka yi jana'izarsa da safiyar Lahadi

  



A hirarsa da BBC, Shiekh Bala Lau ya ce "ba mu san dalilin rubuta wannan labarin ba. Ya kamata a tuntubi iyalinmu ko ƙungiyarmu ta Izala.

"Rayuwa tana da farko kuma tana da karshe kamar yadda Allah ya karbi rayuwar Annabi SAW. Amma bai kamata ace jarida ta dauki labarin da ba ya da tushe ba. Wannan wata kiyayya ce."

A nata bangaren ƙungiyar Izala bayan karyata labarin mutuwar shugabanta, ta bukaci Sahara Reporters ta fito ta gaggauta ƙaryata labarin da ta yaɗa.

Shiekh Isa Ali Pantami, ya ce hotunan da Sahara Reporters ta wallafa na jana'izar Shiekh Adam Muhammad Gashua ne, tare da shawartar kafar ta fito ta gyara.




A hotunan da Sahara ta wallafa ta ce mutane sun taru wajen jana'izar Shiekh Bala Lau inda suka yi watsi da ƙa'idar yin nesa nesa da juna da ake son mutane su yi saboda tsoron bazuwar cutar korona.

Zuwa Yanzu Sahara Reporters ba ta yi ƙarin bayani ba game da labarin da ta wallafa, ko ta nemi gafara. Ko da yake ta goge labarin da ta wallafa a Twitter.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ina nan da rai na - Shiekh Bala Lau Yayi Martani Mai Zafi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?