LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Korona ta sake hallaka mutane biyu a Kaduna
ROHOTON: https://hausa.legit.ng/

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da mutuwar karin wasu mutane biyu da ke jinyar cutar korona, lamarin da ya mayar da adadin mutanen da suka mutu saboda annobar a jihar zuwa mutane uku.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya ce sabbin mutanen biyu da suka mutu sune; wani babban mutum daga karamar hukumar Makarfi da kuma wata mata daga Zaria.

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na tuwita, gwamnan ya ce an sake samun karin mutane biyu da suka kamu da kwayar cutar, lamarin da ya mayar da adadin masu korona a jihar zuwa mutane 87.

A cewar gwamnan, mutane biyun da suka kamu da kwayar cutar sun hada da wani namiji daga karamar hukumar Igabi da wata mace daga karamar hukumar Chikun.A ranar 2 ga watan Mayu aka fara samun mutum na farko da cutar korona ta kashe a jihar Kaduna. Marigayin, tsohon ma'aikacin gwamnati ne, da ya boye gaskiyar cewa ya yi bulaguro zuwa Kano. Ya mutu ne kafin sakamakon gwajinsa ya fito. 


> KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments