--
Majalisa ta jefa kwangilolin cuwa-cuwa a kasafin NDDC – Kemebradikumo Pondei

Majalisa ta jefa kwangilolin cuwa-cuwa a kasafin NDDC – Kemebradikumo Pondei

Shugaban NDDC na rikon kwarya Kemebradikumo Pondei Hoto: The Cable Source: UGC 
ROHOTON: LEGIT.NG

Shugaban NDDC, Kemebradikumo Pondei ya ce an yi cushe a kasafin hukumarsa - Pondei ya zargi majalisa da yin cushen ayyukan bogi a cikin kasafin kudin NDDC Shugaban hukumar NDDC na rikon kwarya, Farfesa Kemebradikumo Pondei, ya jefi ‘yan majalisar tarayya da zargin yin cushe a cikin kasafin kudin NDDC na shekarar bara watau 2019.

Kemebradikumo Pondei ya fadawa manema labarai cewa an cusa kwangilolin bogi kusan 500 a kasafin 2019. Pondei ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 26 ga watan Mayu, 2020. Farfesa Pondei ya bayyanawa ‘yan jarida wannan ne a jihar Ribas,

a matsayin martani game da zargin da ake yi wa shugabannin rikon kwaryar NDDC na yin awon gaba da kudi. Shugaban na NDDC ya ke cewa sun gano ta’adin ne lokacin da su ka binciki kasafin kudin hukumar na 2019. Pondei ya ce ‘yan majalisa sun jirkita kasafin da aka aika masu.

“Mun gano cewa bayan hukumar ta aikawa kwamitin NDDC a majalisar tarayya, ba mu iya gane kundin kasafin kudin da aka dawo mana da shi ba.” Inji Kemebradikumo Pondei.

“An yi wa kasafin kudin 2019 wani irin cushen hauka, inda aka lafta sababbin ayyuka kusan 500 aka dawo mana da su. Mun gano cewa an warewa muhimman ayyukan kudi kadan.” Idan ba ku manta ba shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin a binciki kudin da aka kashe a hukumar NDDC. Wannan zai sa a bankado duk barnar da jami’an hukumar su ka yi.

Sai dai shugaban hukumar mai kula da cigaban Neja-Delta, Farfesa Pondei ya ce babu wani kwangilar kirki da NDDC ta yi. Pondei ya ce an bar hukumar da 'yan kananan ayyuka. Pondei ya nuna takaicinsa game da yadda aka bar hukumar NDDC ta koma gina hanyar ruwa, da kafa karafunan wuta, abin da a cewarsa ko karamar hukuma za ta iya daukar nauyi. A jawabin da ya yi wa ‘yan jarida, farfesan ya ce wadanda su ke tsoron binciken kudin da shugaban kasa ya ce ayi ne su ke zargin kwamitin rikon kwaryarsa da cin kudin hukuma.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Majalisa ta jefa kwangilolin cuwa-cuwa a kasafin NDDC – Kemebradikumo Pondei "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?