LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yadda masu ɗorin karaya na gargajiya 'suke jawo ce-ce-ku-ce a Jigawa'Sakamakon yadda ake takaddama tsakanin likitoci da masu dorin gargajiya kan gyaran karaya, wakiliyar BBC Aisha Shariff Baffa, ta yi nazari a kan haka a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Sabon garin Madora gari ne mai nisan kilomita kusan shida daga karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa, haka kuma gari ne mai yawan mutane kusan dubu biyu.

Da ka shiga garin za ka yi karo da gidan Sarkin Madora Muhammadu Auwalu, inda a kofar gidansa akwai wani dakin kasa wanda shi ne dakin kwantar da masu karaya, wato ga Malam Auwalu Sarkin Ɗori wannan daki daidai yake da dakin kwantar da marasa lafiya a asibiti.

A wannan gari sana'ar dori ba a babba ko karami ko kuma tsoho ta tsaya ba, hatta yaro ko yarinya 'yar shekara 10 zuwa sama ana koya musu ita.

Da wannan sana'a ta dorin gida mutanen wannan gari kanci su sha su yi sutura kai hatta sauran bukatu kamar na aure da dai makamantansu mutanen kan yi.

Mata a wannan gari ma ba a bar su a baya ba domin akwai madora da dama daga cikinsu wadanda yawancinsu kan ce sun gaji wannan sana'a ne tun kaka da kakanni.

Masu dori a wannan gari a lokuta da dama kan yi ikirarin cewa duk munin karaya ko da kuwa za ta gagari likitoci, to su idan aka kawo mutum za su dora shi tsaf har ya mike.

Wani abin ban al'ajabinma madoran kan ce wai a wasu lokuta idan likita zai yi wa mutum aikin karaya a kan gayyato su a shiga da su cikin dakin tiyatar likita ya yi nasa aikin, shi ma mai dori ya yi nasa.

'Babu abin da yake gagararmu'
Haka kuma madoran wannan gari kan ce ko da mutum hadari ya yi kashin wani bangare na kafarsa ko hannunsa ya fita, to idan an kawo musu wannan marar lafiyar, su kan je inda aka yi wannan hadarin su nemo kashin su zo su dora mutum.

Muhammadu Auwalu, shi ne shugaban madoran gari, ya ce, ita wannan sana'a ta dorin gida gada ya yi tun kaka da kakanni, kuma dukkan 'yan garin haka suka gaji wannan sana'a.

Ya ce "Ita wannan sana'a ta mu nada nasaba da kwarewar mutum kuma babu abin da yake gagararmu idan dai a kan karaya ne".

Sarkin dorin ya ce: "Ko da karaya za ta kai shekara goma ko fin haka in dai har za a kawo mana marar lafiya to da izinin Allah za mu gyara shi ya kuma tashi."

Ya ce a rana a kan kawo masa masu karaya ya gyara kusan ashirin koma fin haka kuma daga garuruwa daban-daban.

Muhammadu Auwalu, ya ce saboda iya aikinsa har dakin kwantar da marassa lafiya gare shi, inda idan aka kawo masa marar lafiya daga nesa to ya kan kwantar da shi na tsawon wasu lokuta, idan kuma a kusa ne to yana gama gyara karayar sai mutum ya tafi kawai abinsa.

Ya ce saboda suna mu'amala da likitoci a aikinsu don idan likita ya kasa da karaya yakan tura musu su gyara, to wannan dalili ne ya sa a wasu lokutan su kan siyi kafso ko fanadol maganin rage radadi su bawa marar lafiya saboda ya samu saukin zugin da karayar ta ke.

Sarkin dorin ya ce saboda kwarewarsu, har likitoci kance wai aikin madoran ya fi nasu.

Ya ce "Mu fa a tsarin aikinmu ba ma aikin da za a ce a je asibiti daga baya, sai dai daga asibitin a ce a zo wajenmu".

Muhammadu Auwalu ya ce " A tsawon shekaru hamsin da na shafe ina dorin gida, ban taba yin dorin da aka kai mutum asibiti daga baya ba".

Ya ce a yanzu ya koyawa 'ya'yansa wannan sana'a ta dori saboda gadonsu ce kuma suma suna dora masu karaya da dama.

'Nazo wajen masu dori saboda likitoci sun gaza'

A dakin kwantar da marasa lafiya na tarar da wani marar lafiya wanda yake a zaune kuma kafarsa ta dama a mike an nade ta cikin tsumma tana kuma tsakanin karafuna inda aka daidaita ta.

Na tattauna da shi inda ya shaida mini cewa karaya ya samu a dalilin hadarin babur, da farko ya je asibiti ya shafe kwana sittin ba daya, a nan ne aka gyara masa karaya biyu, gwiwar ce taki dadi.

Ya ce "Da na ga babu sauki ga kuma kashe kudi sai na nemi sallama daga asibiti aka kuma sallame ni, ko da na koma gida jiki yaki dadi sai aka turo ni Sabon garin Madora, kuma Alhamdulillahi ga shi har ina iya lankwasa gwiwata".

Ƙafar 'yata ta zagwanye

To yayin da sarkin dori Muhammadu Auwalu ke tunkahon cewar aikinsu na kyau sai dai idan sumasi aka samu, to da alama an samu sumasin a kan wata da na je na ganta.

Yarinyar da na ba wa suna Binta, sikila ce kuma marainiya wadda ta samu lalurar karaya a hannu, mahaifiyarta ce ke dawainiya da ita.

Mahaifiyar yarinyar ta ce dorin gida ya janyo musu babban tashin hankali saboda yadda hannun Binta ya koma duk sai kashi ba fata.

Ta ce "Saboda rashin kudi na kai 'yata wajen masu dorin gida, amma ga shi yanzu duk fatar hannun ta zagwanye don ko daga hannunta bata yi".

Shin ko likitoci sun gaza a aikinsu ne?
Dakta Mahmud Muhammad likitan kashi ne a asibin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Birnin Kudu ya shaida mini cewa babu wani likitan kashi da ya kware a aikinsa da zai tura marar lafiya wajen masu dorin gida.

Likitan ya ce harkar kashi ba abu ne da ake yinsa ba da ka ba -- misali da zarar mutum ya karye abu na farko da ake masa shi ne a dauki hoton wajen don sanin wacce irin karaya ce.

Ya ce daukar hoton ne zai baka hasken irin aikin da zaka yi wa marar lafiya.

Dakta Mahmud ya ce: "A gaskiya muna fuskantar matsaloli daga marasa lafiyar da suka karye saboda kusan kaso 60 cikin wadanda suka karye a Jigawa dorin gida suke zuwa ana musu, daga baya idan an samu tangarda kuma sai su dawo asibiti bayan an gama jagwalgwala karayar".

Ya ce "Wannan ba karamar matsala ba ce, saboda da tun farko asibitin suke zuwa da yawanci ba za a samu matsalar ba, amma sai abu ya baci sai a rarrafo a taho asibiti".

Sannan game da batun wai suna aiki tare da masu dorin gida kuwa, wannan ba gaskiya bane, domin in dai har likita ya san aikinsa ai ba sai ya nemi daukin kowa ba inji Dakta Mahmud.

To ko me yasa mutane ke zabar dorin gida musamman wadanda suka fito daga karkara?

Mutane musamman mazauna yankunan karkara babbar sana'ar da suka dogara da ita ita ce noma sai kuma kiwo.

To idan tsautsayi ya gifta mutum ya karye abin da ke fara zuwa ran iyalansa shi ne a kai shi wajen masu dorin gida, ganin cewa idan aka je asibiti ana kashe makudan kudade kafin mutum ya warke.

Amma kuma idan dorin gida ne, dan abin da za a kashen bai kai na asibitin ba.

Za a iya cewa, kudaden da asibitocin kashi ke caja idan mutum ya karye suke hana yawancin wadanda suka karye zuwa asibiti don a duba lafiyarsu.

Wannan dalili shi ne ya ba wa masu dorin gida musamman a yankunan karkara ko kuma a gari kamar Sabon garin madora damar cin karensu ba bu babbaka.

A lokuta da dama dai wadanda aka yi wa dorin gida kan gamu da matsala wadda dole sai an koma asibiti.

Kazalika a jiha kamar Jigawa wadda akwai masu karancin ilimin boko da dama, ba lallai su fahimci illar dorin gida ba, haka talauci ma na taka muhimmiyar rawa wajen kin kai wadanda suka karye asibiti, tun da ana ta ciki wake ta karaya.

Wadannan dalilai na daga cikin abubuwan da ke sa ake yawan samum wadanda suka samu matsala bayan sun karye inda a dalilin dorin gida mutane da dama kam rasa hannu ko kafarsu.

Me gwamnatin jihar ke yi don kawo karshen wannan matsala da dorin gida kan haifar?

Kimanin shekaru goma ke nan da gwamnatin jihar Jigawa ta bullo da dokar yi wa masu dorin gargajiya garanbawul, ga kuma abubuwan da dokar ta kunsa:

Yakamata duk wanda zai yi gyaran karaya dole ya samu sahalewar gwamnati ko kuma masu ruwa da tsaki a bangaren karaya.


Sannan dole sai an ba wa duk mai dorin gida izinin fara gyara karayar bayan ya amsa wasu tambayoyi.

Akwai maganar bita, dole sai an yi wa masu dorin gida bita ma'ana an fara basu horo kafin su rinka gyaran karaya.
Dole masu dorin gida su rinka tsaftace inda suke aikinsu.


Abin tambayar anan shi ne shin ko wannan doka na aiki kuwa a jihar ta Jigawa ganin yadda masu dorin ke harkokinsu ba tare da kiyaye wasu ka'idoji ba.

Dakta Kabir Ibrahim, shi ne shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar Jigawa, ya ce yanzu kokarin da ake shi ne a shigo da masu dorin gida cikin harkokin asibiti don su ga yadda ake yi da inda ake samun matsaloli don su kiyaye.

Ya ce, " Akwai kuma horo ga masu dorin gargajiyar da suka yi kunnen kashi, horo na farko shi ne tarar naira dubu biyar tare da jan kunne, sannan akwai matakin da mutum zai kai a tsare shi misali idan yaki sabunta takardarsa ta shaidar ya cancanci ya yi dori wadda gwamnati ta bashi.

Masana dai na ganin idan har za a samar da asibitocin kashi a kusa da al'umma kuma a kan farashin da zasu iya biya tare da wayar musu da kai, za a samu sauki samun matsala sakamakon dorin gida, haka da yanayin da Binta ke ciki ka iya zama tarihi.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments