--
An cafke 'yan fashi 2 masu kwacen keke napep a Anambra

An cafke 'yan fashi 2 masu kwacen keke napep a Anambra

ROHOTON: LEGIT.NG

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Anambra, ta samu nasarar cafke wasu miyagun mutane biyu da ake zargin su da aikata laifin fashi da makami. Majiyar rahoton ta bayyana cewa, wani matukin keke napep, Joseph Asogwa, a ranar Talata ya fada tarkon 'yan fashi da makami a kan hanyar Onitsha zuwa Owerri a da ke yankin Oba na jihar Anambra. Miyagun biyu bayan kwatar abin neman abincin na Joseph,

sun kuma kwarara masa wani tafasasshen ruwa mai radadin gaske, wanda ya makantar da shi na wani dan lokaci. Cikin wannan yanayi na karaji da kururuwa ta neman a kawo masa dauki, ya sanya nan da nan jami'an tsaro masu sintiri a hanyar suka cimma masu ta'adar biyu kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito. Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari. Ya ce an an cafke ababen zargin biyu tare da baburin mai kafa uku.

Ya ce: "Da misalin karfe 7.55 na ranar 26 ga watan Mayun 2020, a yankin Umuogali da ke kan hanyar Onitsha zuwa Owerri, wasu 'yan ta'adda biyu da su ka yi kaurin suna wajen kwacen keke napep, sun shiga hannu." An garkame 'yan ta'addan da suka sharaha da sunan kek a ofishin 'yan sanda na Oba da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra."

A Arewacin Najeriya kuma mun samu cewa, Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, ta kaddamar da bincike kan yawan mace macen da ake samu a jihar a baya bayan nan. Masari ya ba da sanarwar hakan ne yayin gabatar da jawabai a taron manema labarai da gwamnatin jihar ta shirya don sanar da al’ummar jihar halin da ake ciki game da annobar cutar

korona. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito gwamnan yana cewa, jihar Katsina na da kwararru da za su gudanar da bincike a kan lamarin don gano dalilin mace macen da ake samu a fadin jihar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An cafke 'yan fashi 2 masu kwacen keke napep a Anambra"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?