LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Coronavirus a Kano: Kungiyar ƙwadago ta yi tur da Ganduje kan rage albashin ma'aikata

ROHOTON: BBCHAUSA

Ƙungiya ƙwadago ta jihar Kano da ke Najeriya ta yi Allah-wadai da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje bisa rage albashin ma'aikata.

Shugaban ƙungiyar, Kabiru Ado Minjibir, ya shaida wa BBC cewa za su tsunduma yajin aikin gargadi idan gwamnan bai mayar wa ma'aikatan albashin da aka rage musu ba.

A cewarsa: "Mun bai wa gwamnati wa'adin kwana goma sha hudu ranakun aiki - daga yau din nan ranar Laraba 27 ga watan Mayu zuwa ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, gwamnati ta duba bukatunmu ta biya mana su. Idan kuma bata yarda da su ba, to daga ranar Litinin 15 ga watan Yuni, 2020 kafatanin ma'aikatan wannan kungiya za su tsunduma yajin aiki."

Ya musanta rahotannin da ke cewa bakinsu daya da gwamnatin jihar, yana mai kira ga ma'aikata "su yarda da mu, mu kuma bi'izinilLahi ba za mu ci amanarsu ba; za mu yi duk abin da za mu yi wanda doka ta ba mu domin mu tabbatar mun kwato musu hakkinsu."

A makon jiya ne ma'aikatan gwamnatin jihar ta Kano suka yi zargin cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta zaftare musu albashi a daidai lokacin da suke shirye-shiryen ƙaramar Sallah.

Galibin ma'aikatan da BBC ta yi hira da su sun ce an biya su albashi a tsohon tsari - wato kafin a yi karin albashi - kuma an zaftare kashi 10 zuwa 20 cikin 100.

"Albashin ya zo a tsohon tsari na minimun wage; a baya, ina daukar N76, 000 yanzu kuma ya koma N72, 000. Shi mai girma Gwamna ya fadi wadanda za a yi wa ragi, babu wanda aka ambata a cikin ma'aikatan gwamnati aka ce zai samu ragi," a cewar daya daga cikin ma'aikatan da lamarin ya shafa.

Wani kuma ya ce: "Albashi da aka biya gaskiya kusan tsohon albashi aka bayar, ma'ana katrin da aka yi na minimum wage an cire shi gaba daya."

A cewarsu, lamarin ya jefa su cikin halin ƙunci da rashin tabbas, ganin yadda ƙungiyar ƙwadago a jihar ke cewa ba a tuntuɓe ta ba kafin daukar wannan matsaya.

Gabanin hakan, gwamnatin ta sanar da rage wa masu muƙaman siyasa rabin albashi saboda raguwar kuɗaɗen shiga dalilin faɗuwar farashin man fetur sakamakon annobar korona.

Kasashen duniya da dama dai sun rage ma'aikata, yayin da wasu kuma suka rage albashin ma'aikata a yayin da cutar korona take ci gaba da yin mummunan tasiri a kan tattalin arzikin duniya.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments