LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

'Matata ta kwashe shekara 10 tana yi mini fyaɗe'ROHOTON: BBCHAUSA

Rahotanni da dama da suka shafi fyade an fi yawan danganta su da mata. Kashi daya bisa uku na mata sun taba fuskantar fyade da nau'ukan cin zarafi a rayuwarsu kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ba da kididdiga.

Abubuwan da ba a cika magana ba ko kuma bayar da rahoton su ba, su ne cin zarafin maza.

Cin zarafin maza abin ƙi ne a al'ummomi da dama, kuma waɗanda hakan ya shafa suna gwagwarmayarsu su kaɗai ba tare da samun taimako ba.

Wani matashi daga ƙasar Ukraine ya yi wa BBC karin bayani dangane da abin da ya fuskanta inda ya ce a sakaya sunansa. Ga abubuwan da ya shaida mana da kuma shawarwari kan alamomin da za a iya gane cin zarafi.

A karon farko:

Ban sani ba ko abokai na sun zargi wani abu. Mutane na kallon komai lafiya daga waje: ana wasa da dariya da nishadi da komai na more rayuwa. Mun zagaye kusan kasashen duniya tare.

Ba na tsoranta idan mun yi tafiya: ba ta cin zarafi na gaban sauran mutane. Babban abin da nake yi shi ne na guji mu zauna mu biyu

Sai a cikin 'yan kwanakin nan na gane cewa tsohuwar matata ta shafe shekaru 10 tana mani fyade.

Ira ce matata ta faroko. Mun hadu dokacin muna 'yan shekaru 20 da wani abu - kuma ita ce ta ce tana so na.

Iyayena suka matsa mani dole sai na bar gidansu sakamakon na fara soyayya da wata. Ma'ana idan na gfara soyayya dole na bar gidan iyayena na fara sabuwar rayuwa, a rana daya na rasa komai.

Abin ya bani tsoro. Zan iya zama da ita ne kawai idan na tara kudi.

Kaskantar da kaina
Dangane da haka, na zama abin kunya wurin mahaifiyata da kuma yadda na koma - na kaskantar da kaina.

Jima'i na na farko da Ira na fara yi a rayuwata, duk da na so haka. Sai dai hakan bai yi mani daidai ba, jima'in ya yi mani zafi.

Jima'in da muka yi na farko mun shafe sa'o'i biyar muna yi, kuma na cutu duk a wannan lokaci.

Tana da wani tunani na cewa dole sai na fitar da maniyi kafin ta kyale ni, sai da ta yi ta taba ni har hakan ya faru. Hakan yana daukar kusan awa daya zuwa biyu.

Ana jima'i ne domin a ji dadi amma ni ban taba jin dadinsa ba. Ban saba da yin jima'i ba, duk a tunanina wahala ake sha a wannan harka.

Amma ba da dadewa ba, sai na ce ''A'a,'' amma hakan bai sa ta daina ba. Ta hakan ne ya zama ta fara yi mani fyade.

Na shiga tarko
Hakan ya sa na yi doguwar tafiya zuwa kasar waje domin yin kasuwanci. Ina tsoron rasa Ira, wannan ne ya sa na nemi ta biyo ni. Na yi kokarin mu yi aure da ita, amma ta ki yarda, amma duk da haka ta biyo ni. Daga nan ne aka fara.

Na dawo aiki na gaji ina so na huta, amma sai ta fara neman da mu yi jima'i. Na yarda da hakan a karon farko da na biyu a kullum sai ta koma ta ce tana so mu yi, sai na ce mata A'a.

Hakan ke saka wa tana duka na kuma babu abin da zan iya yi. Tana amfani na ƙumbar yatsunta inda take kartar jikina har sai ya fitar da jini, wani lokaci ma har naushi na take - amma bata ji mani ciwo a fuska sai dai tana cutar da ni ne a inda ke boye a jikina kamar kirjina da baya da hannuwa na.

Bana dukanta sakamakon ina tunanin dukan mace ba daidai bane. Haka iyayena suka tarbiyantar da ni.

Ina jin kaina kamar wani karamin yaro, domin na kasa guduwa. Tana samun abin da take so kuma ita ce ke morewa.

Na yi kokarin kama daki a wani otel amma ban iya yaren da suke yi ba, sun kasa gane me nake so na fadi, a haka ma na kara fadawa wani tarko.

Na ji tsoron komawa otel ko da na tashi aiki, hakan ya sa na yi ta gararamba cikin kasuwa har lokacin tashi.

Bayan nan sai na ci gaba da yawo cikin gari cikin sanyi ga shi ban da kayan sanyi.

Hakan ya sa na samu ciwon mafitsara da masassara. Duk da haka Ira ba ta daina mani fyade ba: Dole na yi abin da take so.

Na yi kokarin rabuwa da ita amma abin ya gagara
Na koma zama da iyayena da kokarin yanke alakata da Ira, amma duk kokarin da na yi na yanke hulda da ita na shekaru ya ci gaba a haka.

Za mu yi fada, na kashe wayata, na boye amma duk da haka za ta zo ta bani hakuri tare da yin alkawarin komai ya wuce ba zai sake faruwa ba.

Kuma a kullum ina kokarin komawa domin ci gaba da zama da ita.

Tun a farko na yi kokarin rabuwa da ita amma a karshe na kasa. Ta tilasta mani kan cewa dole sai na aure ta kuma mun yi auren duk da ba a son raina ba.

Yadda na samu mafita
Wata rana lokacin damina, ina kwance kan gado masassara da ciwon kirji sun kwantar da ni.

Babu wanda ya zo domin duba ni duk a lokacin. A lokacin ne na gane rayuwata ba ta da amfani a wurin jama'a kuma babu wanda zai zo domin ya duba ni ko da na mutu.

Lokacin na shiga wani hali na tsoro da tashin hankali kuma na zama abin tausayi. Na yi kokarin fada wa wani amma ban san wanda zan fada wa ba.

Wani lokaci nakan je gidan iyayena idan ba su nan domin na zauna ni kadai.

A karshe dai sai na samu wani likita mai ilimin kwantar da hankali da bada shawarwari wanda ya taimaka mani. Ni da Ira mun samu kowa ya bayyana abin da ke cikinsa kuma a lokacin da nake bayani an hana ta ta katse ni daga bayani na.

A wannan lokaci ne na fara magana kan cin zarafin da take yi mani.

Ta nuna bacin ranta tana ta ihu inda take cewa ba gaskiya bane.

A lokacin sai ta nemi mu rabu, kuma na san ba son haka take yi ba. Ina tunanin ta yi kokari ne domin ta rufe mani baki. Na san bazan samu dama irin haka ba, wannan ne ya sa na yarda mu rabu.

Kuma a karshe mun rabu.

Ko a ranar da na saka hannu kan takardar rabuwa, ita ce rana mafi farin ciki a gareni.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments