LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kun yi ma na aringizo - Gwamnatin Zamfara ta musanta NDDC a kan alkaluman ma su koronaROHOTON:LEGITHAUSA.NG

A ranar Talata ne gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana rashin amincewarta da alkaluman da NCDC ta fitar na wadanda su ka kamu da cutar korona a jihar ranar Litinin. A ranar Litinin ne NCDC ta sanar da cewa sabbin mutane 10 sun kamu da cutar korona a jihar Zamfara. Kwamishinan lafiya a jihar Zamfara, Alhaji Yahaya Kanoma, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa mutane biyu ne aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar korona a jihar Zamfara ranar Litinin.


Kwamishinan ya bayyana cewa tuni gwamnatin jihar Zamfara ta ankarar da NCDC a kan kuskuren da ta yi tare da neman ta gyara cikin gaggawa. "Mun yi matukar mamaki bayan ganin alkaluman NCDC sun nuna cewa an samu sabbin mutane 10 da su ka kamu da cutar korona a Zamfara bayan mutane biyu kacal mu ka sani.
SHUGABAN NCDC A NIGERIA

"Sakamakon da aka dawo ma na da shi daga NCDC ya nuna cewa mu na da jimillar mutane 76 da ke dauke da cutar, an sallami 45 daga cikinsu, 26 su na cibiyar killacewa, mutane biyar sun mutu, ba mu san inda NCDC ta samo karin mutane 8 da su ka sanar ba.

"Mun tuntubi NCDC amma sun kasa ba mu wani bayani da zai gamsar da mu, a saboda haka mun nemi su rubuto ma na takardar neman afuwa tare da daukan alkawarin za su fitar da sanarwar janye aringizon da su ka yi ma na," a cewar kwamishinan. Kwamishinan ya ce jihar Zamfara ta kammala shirin samar da cibiyar gwajin cutar korona, abinda kawai ya rage shine ziyara da amincewar NCDC.

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/Post a comment

0 Comments