LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kano: Shugaban majalisar limamai, Falalu Dan Almajiri, ya rasu

Allah ya yi wa shugaban majalisar limamai na jihar Kano, Falalu Dan Almajiri rasuwa - Kamar yadda majiya daga iyalansa ta bayyana, ya rasu a yau Talata, 19 ga watan Mayu

Falalu Dan Almajiri tsohon shugaban majalisar zartarwa ta walwalar alhazai ne a jihar Kano Sanannen malami kuma shugaban majalisar limaman jihar Kano, Falalu Dan Almajiri, ya rasu. Marigayin limamin ya rasu ne a sa'o'in farko na yau Talata, 19 ga watan Mayun 2020.

Wata majiya daga iyalansa ta ce ana shirye-shiryen birne marigayin a halin yanzu, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito. A watan Nuwamban 2018, Dan Almajiri ya yi murabus a matsayin shugaban majalisar zartarwa ta hukumar walwalar alhazan jihar Kano, sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Tun daga bullar annobar korona a kasar nan, ana ci gaba da fuskantar mace-mace a jihar Kano ballantana a tsakanin dattawa. Duk da har yanzu a hukumance babu wata alaka da ta danganta mace-macen da annobar, akwai zargi mai matukar karfi da ke dangana hakan da cutar COVID-19 a jihar.

A wani labari na daban, a kalla mutum 197 ne wadanda ake zargi da laifuka daban-daban da ya hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, satar motoci da kwacen adaidaita ne suka shiga hannun 'yan sandan jihar Kano.

An kama wadanda ake zargin tsakanin ranar 11 ga watan Mayu zuwa 15 ga watan Mayu a yankuna daban-daban na jihar. Rundunar Operation Puff-Adder ne suka yi wannan kamen.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, jami'in hulda da jama'a na rundunar ya bayyana hakan ga manema labarai a yammacin Juma'a. Ya ce wannan babban ci gaba ne da aka samu. Ya ce, daga cikin wadanda ake zargin, akwai 'yan fashi da makami 12, masu garkuwa da mutane 5 sai kuma 'yan daba 115. Bakwai daga ciki masu kwace ne wadanda aka kama da motoci hudu, adaidaita sahu biyu, babura bakwai da kekuna biyu.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments