LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Coronavirus: An tsawaita dokar kulle a Kano da mako biyuKwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar korona ya sanar da cewa an tsawaita dokar kulle a Kano da mako biyu biyo bayan ƙarewar wa'adin dokar a yau Litinin.

Boss Mustapha, shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnati, shi ne ya sanar da hakan a wurin taron manema labarai na kullum kan matakan daƙile cutar korona ranar Litinin a Abuja.

Kazalika su ma matakan nesa-nesa da juna da aka ɗauka da suka haɗa da zirga-zirga tsakanin jihohi an tsawaita su da mako biyu.

Rahoton da ta bayar a daren Lahadi, ma'aikatar lafiya ta Kano ta ce mutum 64 ne suka harbu da cutar a cikin sa'a 24 da suka wuce, yayin da aka sallami 18 sannan ɗaya ya rasu.

Matakin tsawaita dokar na zuwa ne yayin da ake sa ran yin bikin Ƙaramar Sallah ranar Asabar ko Lahadi sakamakon gama azumin Ramadana.

Yanzu haka mazauna binin Kano na iya fita domin sayayyar kayan abinci a ranakun Litinin da Alhamis, abin da ke nufin indai za a bar mutane su je sallar idi to sai an sauya ranakun sassauncin.

Duk da sassaucin fita na kwana biyu da mutanen Kano ke da shi, haramcin taruka da suka haɗa da na addini na nan daram.

kuma mazauna yankunan sun je masallatan Juma'a da majami'u tun daga ranar Juma'a.

Wannan ne mako na huɗu da jihar ta Kano ta kasance a kulle, sakamakon annobar korona.


Adadin masu cutar korona da aka samu a Kano ya kai 825, inda jihar ke biye wa Jihar Legas wadda ke da kusan kaso ɗaya cikin uku na yawan masu cutar a Najeriya.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/Post a comment

0 Comments