LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Talaucewa zanyi idan nace zan taimakawa talakawa – Dino MelayeTsohon sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya mayar da martani akan masu kalubalantar kan cewa ya sayar da manyan motocinshi ya taimakawa talakawan dake kusa da shi.

A wani bidiyo da ya saki a yau da safe, Dino Melaye ya bayyana wannan magana ta su a matsayin mugunta, inda ya ce maimakon sayar da motocinshi, yanzu haka yana cigaba da addu’a Allah ya bashi kudi ya karo wasu motocin da gidaje, saboda sune abubuwan da yake so a rayuwarshi.

A cikin bidiyon Dino Melaye ya ce ba zai iya sayar da kadarorin shi ba saboda kawai ya taimaki talakawa, inda yace masu kudi ne kawai zasu iya taimakar talakawa, ya kara da cewa da mutum ya zama talakawa shikenan kuma shima ba zai iya taimakawa wasu ba.

Dinoa Melaye ya bayyana cewa shi ba zai iya kawar da matsalar kowanne mutum ba, Allah ne kawai zai iya kawar da matsalolin mutane.
Ga dai bidiyon maganar tashi a kasa:
 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments