--
Kotu ta hana malamin addinin Musulunci auren matashiya mai shekaru 16

Kotu ta hana malamin addinin Musulunci auren matashiya mai shekaru 16

Wata kotun sauraron matsalolin da su ka shafi iyali da ke zamanta a jihar Ondo ta dakatar da wani malamin addinin Musulunci, Yusuf Lateef, daga auren wata matashiya mai shekaru 16 ( an sakaya sunanta). Tun a shekarar 2019 Malam Lateef ya tuntubi iyayen yarinyar tare da bayyana niyyarsa na son aurenta, amma sai yarinyar ta ki amincewa. Jaridar Punch ta rawaito cewa iyayen yarinyar sun tursasata amincewa da bukatar Malam Lateef tare da saka lokacin bikinsu.

Binciken jaridar Punch ya gano cewa matashiyar ce mace ta tara da Malam Lateef zai aura. Domin nuna rashin amincewarta, yarinyar ta gudu daga gidansu da ke karamar Odigbo zuwa wurin dan uwanta da ke Akure, babban birnin jihar Ondo, a ranar da za a daura aurenta da Malam Lateef. Matashiyar ta mika korafinta ga ma'aikatar harkokin mata da inganta zamantakewa, inda ta samu mafaka ta wasu kwanaki.

Daga ma'aikatar ne aka dauki maganar zuwa wata kotun sauraron matsalolin da su ka shafi iyali da ke Akure, inda aka gayyato Malam Lateef da iyayen yarinyar domin tuhumarsu da saba dokar hakkin yara da jihar Ondo ta kirkira a shekarar 2007.

Bayan jin korafin mai kara, alkalin kotun, Majistare Aderemi Adegoroye, ya yanke hukuncin cewa a mayar da yarinyar gidan iyayenta tare da umartar Malam Lateef ya saka hannu a kan yarjejeniyar cewa ba zai kara shiga sabgar matashiyar ba.

Kazalika, kotun ta umarci iyayen yarinyar su tabbatar sun cigaba da ba ta kulawa tare da daukan nauyin dawainiyar karatunta. Kwamishinar harkokin mata da inganta zamantakewa a Ondo, Titilayo Adeyemi, ta bayyana hukuncin a matsayin nasara ga yarinyar da kuma jiha.

"Mun ji dadin yadda aka kawo karshen matsalar. Hakan zai zama tamkar gargadi ga duk ma su son aurar ko auren kananan yara a jihar Ondo. "Yi wa karamar yarinya aure tamkar tauye rayuwarta ne. Dole mu tabbatar da cewa mun inganta goben yaranmu mata," a cewar kwamishinar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kotu ta hana malamin addinin Musulunci auren matashiya mai shekaru 16 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?