--
Covi-19: Ba za a yi taron sallar Idi a Abuja ba

Covi-19: Ba za a yi taron sallar Idi a Abuja ba

Hukumomi a Abuja, babban birnin Najeriya, sun umarci mazauna garin musamman Musulmai da su gudanar da sallar Idi a gidajensu saboda yaƙin da ake yi da annobar korona.

Wata sanarwa da Anthony Ogunleye, sakataren yaɗa labaran hukumar FCTA, ya fitar ranar Juma'a ta ce umarnin ya biyo bayan wanda fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ta yi ne cewa kowa ya yi sallah a gida da iyalinsa.

Sanarwar ta ƙara da cewa: "Hakan ya biyo bayan umarnin da kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da annobar korona ya bayar na cewa dukkanin wuraren ibada su ci gaba da kasancewa a rufe a Abuja da sauran wuraren da cutar ta yi ƙamari."

Kazalika FCTA ta ce ta yi wata tattaunawa ta musamman da ƙungiyar limamai da kuma ta Kiristoci wato CAN a Abuja domin tabbatar da cewa an bi

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Covi-19: Ba za a yi taron sallar Idi a Abuja ba"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?