LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Idi: Buhari da gwamnoni sun kulla yarjejeniya biyar a kan bude masallatai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi sun kulla yarjejeniya a kan mataki na gaba don yakar cutar korona

A wani taro da suka yi a ranar Alhamis, sun amince da cewa wuraren bauta ba za su dauka jama'a fiye da 50 ba kuma dole sai da takunkumin fuska - Sun kulla yarjejeniya biyar din ne a yayin da ake ta fama da fargabar bude wasu wuraren bauta bayan isowar sallah karama

A yayin da ake ci gaba da tsoron yaduwar annobar korona sakamakon dage dokar hana sallar jam'i, shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni sun yi taro a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayu.

A nan ne kuwa suka kulla yarjejeniya biyar a kan yadda za a ci gaba da yakar annobar korona a kasar nan. Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnoni shida na yankin arewa da suka hada da Gwamna Ganduje na jihar Kano sun dage dokar hana jam'i a jihar don samu a yi sallar Idi. Jama'a da yawa sun kalubalanci wannan matakin don ya saba wa shawarar kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona da kuma hukumar NCDC.


A ranar Juma'a, 23 ga watan Mayu, shugaba Buhari da kungiyar gwamnoni sun yi taro inda suka amince da bude wuraren bauta tare da yin sallar jam'i amma kada a zarta mutum 50. Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya tabbatar da cewa yin taron har da kungiyar Kiristocin Najeriya.

Fayemi ya samu zantawa da shugaban majalisar koli ta addinin Musulunci, Sultan Sa'ad Abubakar IIi a kan dage dokokin takaita zirga-zirga da kuma na hana zuwa wuraren bauta.


Gwamnonin sun aminta da cewa ba a sauya dokar hana taron jama'a ba, kuma babu gwamnan da zai karya wannan dokar. A wani gefe na daban, wani gwamna daga yankin arewa maso yamma ya bayyana cewa yarjejeniyar da suka zartar da shugaban kasar ya shafa Kiristoci da Musulmai.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments