LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kasar Saudi Arabia bata ga watan Shawwal ba

Gwamnatin kasar Saudi Arabia ta bayyana cewa sai ranar Lahadi za a gudanar da sallar Idin karamar sallah. Ta sanar da hakan ne bayan rashin ganin jinjirin watan Shawwal da aka yi a ranar Juma'a.

Wannan sanarwar na kunshe ne a cikin wata takarda da shafin masallacin Harami na Makka da Madinah ya wallafa a shafinsa na twitter.

"Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a yammacin ranar Juma'a bayan duban tsanaki," wallafar tace.

Ana fara duba watan Shawwal ne a yayin da watan Azumin Ramadan ya cika 29, a hakan ne wasu lokutan ya ke zarcewa ya kai 30.

Wannan sanarwar na zuwa ne bayan kwanaki biyu da masana ilimin taurari suka tabbatar da cewa ba za a ga watan Shawwal ba a ranar Juma'a.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewawata zai riga rana faduwa a ranar Juma'a, saboda haka sai ranar Lahadi za a yi Idin karamar sallah.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments