--
Ke duniya: Mahaifi ya gudu ya bar tagwaye mannannu bayan mutuwar mahaifiyarsu

Ke duniya: Mahaifi ya gudu ya bar tagwaye mannannu bayan mutuwar mahaifiyarsu



Wani direban tasi mai suna Anayochukwu Njoku daga yankin Ehime Mbano ya tsere tare da barin matarsa bayan ta haifi tagwaye a manne. Matar Njoku mai suna Chidinma ta haifi mannannun tagwaye ne a ranar 11 ga watan Maris din 2020 amma kuma Njoku ya ce ba zai iya ganinsu ba. Tagwayen masu suna Goodluck da Rejoice sun rasa mahaifiyarsu bayan sa'o'i uku da aka haifesu.

Halin da jariran ke ciki ne ya ja hankalin wata gidauniyar tallafi a jihar Imo inda suka tsananta kokarin rabesu. Darakta Janar din gidauniyar, Beulah Chukwuma, wacce ta zanta da manema labarai ta ce bayan an birne mahaifiyar yaran, sai aka kawo musu tagwayen. Chukwuma ta ce bayan kokarin gwamnatin jihar na ganin an raba tagwayen, gidauniyarsu ta mika kokon baranta ga kungiyoyi masu yawa don neman tallafi.

Chukwuma tace, "A halin yanzu, muna da tagwayen da ke manne da juna. Mahaifiyarsu mai suna Chidinma Njoku ta rasu a ranar 11 ga watan Maris din 2020, sa'o'i uku bayan haihuwarsu a asibitin Umuokoto Nekede da ke karamar hukumar Owerri ta yamma.

"Mahaifinsu mai suna Anayochukwu Njoku ya tsere ya bar yaran. Bayan isar lamarinsu gaban Gwamna Hope Uzodinma, ya bada umarnin gaggawa a kan kula da walwalar tagwayen. "A halin yanzu, muna kokarin ganin an raba su domin su fara rayuwarsu daban-daban."

Chukwuma ta ce baya ga tallafin da gwamnati ta bada, muna bukatar tallafin jama'a. "Za mu samu tallafi daga jama'a sannan mu kara da na gwamnatin," tace. A wani labari na daban, wata matar aure mai shekaru 18 mai suna Salma Hassan da ke karamar hukumar Itas Gadau ta jihar Bauchi ta shiga hannun 'yan sandan jihar sakamakon zarginta da ake da sokawa mijinta wuka.

Ana zargin Salma ta kashe mijinta mai suna Mohammed Mustapha ne a kan auratayya. Salma, yayin da ta shiga hannun 'yan sandan hedkwata da ke Bauchi, babban birnin jihar a ranar Alhamis, ta ce ta soka wa mijinta wuka ne saboda ya takurata dole sai ya kwanta da ita a daren.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ke duniya: Mahaifi ya gudu ya bar tagwaye mannannu bayan mutuwar mahaifiyarsu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?