LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Gabas ta tsakiya: ​Isra’ila Ta Zargi Iran Da Kai Mata Hari Ta Hanyar Yanar GizoGwamnatin Isra’ila ta zargi kasar Iran da kai mata hari ta hanyar yanar gizo.

(ROHOTON ABNA24.com) Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahotanni da ke cewa, a cikin makonni biyu da suka gabata an kai munanan hare-hare a kan Isra’ila ta hanyar yanar gizo, tare da lalata wasu bangarori da suka shafi ayyukanta.

Rahoton ya ce Isra’ila ta kasa gane ko da ina ne aka kawo mata harin, amma dai ta dora alhakin hakan kan Iran, inda ta bayyana wannan hari na yanar gizo da cewa shi ne mafi muni da aka taba kai mata.

Tun kafin wanann lokacin dai Isra’ila ta sha zargin Iran da cewa tana yi mata kutse a cikin tsarin ayyukanta a yanar gizo, da hakan ya hada da leken asiri da kuma yi mata barna a wasu bangarori da take adana bayanai a yanar gizo.

Iran dai ba ta ce komai kan batun ba, amma kuma ba ta kore cewa tana kai irin wadannan hare-hare a kan Isra’ila ta hanyar yanar gizo ba.KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments