LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Covi-19: Ana Samun Ci Gaba A Fada Da Cutar Corona A Iran

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran ta bakin kakakinta ce ta sanar da alkaluman wadanda su ka kamu da kuma rasuwa daga cutar ta corona a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata, wanda ya ke nuni da samun koma baya idan aka kwatanta da yadda ta kasance a baya.


(ROHOTON ABNA24.com) Ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran ta bakin kakakinta ce ta sanar da alkaluman wadanda su ka kamu da kuma rasuwa daga cutar ta corona a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata, wanda ya ke nuni da samun koma baya idan aka kwatanta da yadda ta kasance a baya.

Kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran Kianush Jahanpur ya bayyana cewa; Adadin wadanda su ka kamu da cutar a cikin sa’o’i, 24 da su ka gabata, sun kai dubu daya da dari biyar da ashirin da tara.

Hakan ya kawo jumillar adadin wadanda su ka kamu da cutar sun kai dubu dari da shida, da dari biyu da ashirin, yayin da wadanda su ka mutu kuwa su ka kai 48.

Daga bullar cutar zuwa yanzu adadin wadanda cutar ta kashe a cikin kasar sun kai 6,589.

Kakakin ma’aikatar kiwon lafiyar na Iran ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka warke daga cutar sun kai dubu 85 da 64.KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments