--
'Yadda na rasa mahaifiyata da kanwata da kawuna a dare daya a Kano| Inji matashi Sadiq Salisu

'Yadda na rasa mahaifiyata da kanwata da kawuna a dare daya a Kano| Inji matashi Sadiq Salisu



ROHOTON: https://www.bbc.com/hausa

Jahar Kano da ke arewacin Najeriya ta fuskanci yawaitar mace-mace a 'yan makonnin da suka gabata, inda bincike ya nuna cewa mafi yawan wadanda ke mutuwar tsofaffi ne kuma mutuwar na zo musu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

To sai dai abin da bincike bai tabbatar na shi ne ko mace-macen na da alaka da annobar cutar Korona ko a'a? Da kuma dalilin da ya sa asibitoci ba sa karbarsu a lokacin da rashin lafiya ta kama su?

Wakilin BBC, Jabir Mustapha Sambo ya tattauna da 'yan uwan wasu daga cikin mamatan don jin halin da suka tsinci kansu kafin da kuma bayan rasuwar 'yan uwan nasu.

Na rasa mahaifiyata da kanwata da Kawuna a rana daya


Sadiq Salisu ya rasa mahaifiyarsa da kanwarsa da kuma kawunsa duka a cikin kwana daya. "Mahaifiyata mai shekaru 72 ta rasu bayan fama da zazzabi mai zafi a gidanta, bayan da aka gaza samun asibitin da zai karbe ta.

Yayin da muke tsaka da wannan juyayi na rashin mahaifiya, kwatsam sai ga labarin rasuwar kanwata da kawuna."

Wani abu mai kara ta da hankali shi ne irin yadda Sadiq ya ga ana tururuwa da gawawwaki a makabartar da aka binne mahaifiyar tasa da ke Gwauron-Dutse.

'Yata ta mutu saboda rashin likitan da zai karbe ta




A wata anguwar ta daban duk dai a cikin kwaryar birnin na Kano, Uwani Umar Musa ita ma ta rasa yar'ta Zara'u bayan fama da zazzabi da ciwon kirji.

Babban abin da ya fi tsayawa Uwani a rai, "bai wuce yadda aka rasa likita ko ma'aikacin jinya da zai kawowa Zara'u daukin gaggawa ba, duk da mun shafe kusan kwanaki biyu a asibiti."

Haka Uwani ta rika kai komo wurin ma'aikatan asibitin, yayin da Zara'u ke kukan numfashinta na kokarin daukewa. A karshe dai ta ce ga garinku nan.

Tsoron korona ya hana asibitoci karbar mahaifinmu har ya mutu


A nan kuma Umar Baban Turai ne ke bayyana yadda ya rasa mahaifinsa mai shekaru 65, bayan gajeruwar rashin lafiya.

"Na fahimci cewa tsoron ko mahaifina na dauke da cutar korona ya sa asibitoci ke gudun karbarsa, Kuma akan haka ne muka yanke shawarar tuntubar hukumar dakile yaduwar cutuka.

Sai dai duk da haka su ma sun yi biris da batun kawo mana agaji har rai yayi halinsa."

Kamar yadda Sadiq ya shaida gawawwaki birjik a makabarta, abin da shi ma Umar ya gani ya girgiza shi.

Sai da muka gaji da haka kaburbura saboda yawan mace-mace


A hira da BBC, wani mai aikin gina kaburbura a makabartar Dandolo ya gazgata abin da jama'ar gari ke fada. A cewarsa "sama da shekaru 30 ina wannan aiki, amma ban taba ganin abin da na gani bana ba.

Mun binne kusan gawa 40 a wuni daya. A yanzu ta kai ga ba mu da karfin gina kaburbura saboda gajiya."

Wannan kadan ne daga cikin gwamman rahotannin mace-macen da aka samu a jahar Kano a 'yan makonnin da suka gabata, wadannda suka ja hankalin jama'a da ke ciki da wajen Najeriya.

Gwamna Ganduje ya zargi gwamnatin tarayya


To sai dai an zargi gwamnatin jihar da tarayya da nuna gazawa.

A hira da BBC Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zargi gwamnatin tarayya da yin ko oho da ibtila'in da ke faruwa a jaharsa.

A cewar gwamnan ya tuntubi mukarraban gwamnati da yake tunanin za su taimaka amma shuru kake ji.

To sai dai a jawabin da ya yi wa 'yan kasar na baya bayannan kan cutar korona, shugaba Muhammadu Buhari ya saka dokar kulle a duk fadin jahar Kano, da kuma shan alwashin kai wa karshen halin da jahar ta sami kanta.

Abin da kwamiti ya gano


'Yan kwanaki bayan jawabin shugaban ne wata tawagar masana harkar lafiya daga gwamnatin tarayyar a karkashin jagorancin Dr Nasir Sani Gwarzo ta isa birnin na Kano.

Dr Gwarzo ya fadi cewa tawagar tasu na fatan shawo kan lamarin annobar cutar korona da kuma mace-macen da ya addabi mahaifar tasa.

A bincike da wata kungiyar likitoci mata ta gudanar kan mace-macen a jahar Kano, ta gano cewa mutun 183 sun mutu a cikin kwanaki kalilan.

Kuma a tattaunawar da likitocin su kayi da 'yan uwan mamatan, sun fahimci cewa mafi yawancinsu tsofaffi ne, kuma sun mutu ne bayan fama da zazzabi mai tsanani, da toshewar numfashi da kuma gudawa.



To amma duk da binciken nasu bai tabbatar da cewa cutar korona ce ta kashe su ba, a cewarsu yanayin jinyar da suka yi ba shi da bambanci da na masu cutar korona.

Wani abu da suka gano kuma shi ne karancin asibitoci da kuma gwaji, wanda hakan ke nuna cewa akwai yiwuwar cutar ta bazu cikin al'umma.

Jahar Kano ce babbar cibiyar kasuwanci a arewacin Najeriya.

Da yawa na ganin cewa matsawar aka yi jinkirin shawo kan matsalar da jahar ke ciki, hakan zai yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin yankin.

A yanzu ba al'ummar jahar Kano kadai ba, har makwabtan jahohi na kwana ne da ido daya a bude, sanin cewa duk abin da ya ci doma ba zai bar awai ba.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 




0 Response to "'Yadda na rasa mahaifiyata da kanwata da kawuna a dare daya a Kano| Inji matashi Sadiq Salisu"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?