LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Amurka Ta Ki Amincewa Da Shirin MDD Na Kawo Karshen Yake-yake A DuniyaA jiya Juma’a ne dai Amurka din ta yi kememe ta ki yarda da daftarin kudurin da aka bijiro wa da kwamtin tsaron MDD na ganin an kawo karshen duk wani yaki da ake yi a duniya, domin a mayar da hankali wajen yakar cutar Corvid-19.

(ROHOTON ABNA24.com) A jiya Juma’a ne dai Amurka din ta yi kememe ta ki yarda da daftarin kudurin da aka bijiro wa da kwamtin tsaron MDD na ganin an kawo karshen duk wani yaki da ake yi a duniya, domin a mayar da hankali wajen yakar cutar Corvid-19.

Matsayin na Amurka ya zo bayan sa’o’i kadan da ta nuna ta amince da hakan.

Watanni biyu aka dauka ana tattaunawa domin fitar da daftarin kuduri na bai daya akan kawo karshen yake-yake a duniya, lamarin da ya sa jami’an diplomasiyya su ka yi mamakin matsayar Amurkan dangane da hakan.

Majiyar diplomasiyya ta bayyana cewa; Amurkan ta nuna kin amincewa ne da kalaman da aka yi amfani da su wajen bayyana hukumar lafiya ta kasa da kasa ( WHO) da ba su yi wa Amurkan dadi ba.

Amurka ta yi bazaranar hawa kujerar naki, matukar aka ambaci sunan hukumar lafiyar ta duniya, yayin da kasar Sin, ta ce idan har ba a ambaci wannan kungiyar ba, to ita ma za ta hau kujerar naki.

A cikin watannin bayan nan na bullar cutar “Corona” Majalisar Dinkin Duniya ta bakin babban magatakardarta ta ke yin kira da a kawo karshen yake-yake a duk fadin duniya saboda a mayar da hankali wajen fada da cutar “Corona”


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments