--
WATA SABUWA: An Sake Tsintar Gawar Wani Mutum A Cikin Birnin Kano!!!

WATA SABUWA: An Sake Tsintar Gawar Wani Mutum A Cikin Birnin Kano!!!



Har yanzu tsugune bata kare ba, sakamakon an cigaba da samun mace macen jama’a da dama a jahar Kano ba tare da an san takamaimen abin da ke kashe su ba.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito an sake tsintar gawar wani mutumi a karkashin gadar Kwankwasiyya dake kofar Nassarawa a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu.

Sai dai ba’a tabbatar da wanene mamacin ba, amma hankulan jama’a sun tashi yayin da mutumin wanda shekarunsa sun kai sittin ya yanke jiki ya mutu a daidai kasar gadar.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa duk kokarin da suka yi na kiran jami’an tsaro da jami’an kiwon lafiya don dauke gawar mutumin ya ci tura.

Hankulanmu sun tashi, ba mu san abinda ya kashe shi ba, mun dai tsinci gawarsa kwance a kasa, mun kira ma’aikatar kiwon lafiya da Yansanda tun da rana, amma babu wani bayani daga wajensu, a yanzu har gawar ta fara kumbura.” Inji shi.

Daga inda wannan lamari ya auku zuwa ofishin hukumar kwana kwana ta jahar Kano bai wuce tazarar mita 100 ba, amma ta gagara aika jami’anta don su ga abin dake faruwa a wurin.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "WATA SABUWA: An Sake Tsintar Gawar Wani Mutum A Cikin Birnin Kano!!!"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?