--
COVID 19: An kama mutum 986 da suka saba dokar kulle a Kaduna

COVID 19: An kama mutum 986 da suka saba dokar kulle a Kaduna




Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama mutum 986 da suka saba dokar hana fita da hana cudanya da mutane a jihar. Rundunar ta ce mutum 48 daga cikin wadanda ake zargin malaman addini ne da masu dandalin shan giya a jihar kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Kwamishinan yan sandan jihar,


Umar Musa Muri, wanda ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a ranar Laraba ya ce an gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu. Ya ce an yi kamen ne domin tabbatar da bin dokar da gwamnatin jihar ta saka na hana fita da dena cudanya da aka saka tun ranar 26 ga watan Maris. 


Ya ce, "Rundunar yan sandan a yunkurin ta na tabbatar da dokar hana cudanya da hana fita da gwamnatin Kaduna ta saka tun ranar 26 ga watan Maris na 2020 domin dakile yaduwar annobar COVID 19 ta kama mutum 986 a sassa daban na jihar. 



"Daga cikin wadanda aka kama, mutum 48 mafi yawanci malaman addini ne da kuma masu gidajen sayar da giya kuma tuni an gurfanar da su gaban kuliya." 


Kwamishinan yan sandan ya kuma yi bayanin cewa rundunar ta kama wasu mutum 91 da ake zargi da aikata laifuka daban daban da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, fyade, sata da wasu laifukan. 



Ya ce an kwato makamai da dama daga hannun mutanen da ake zargi da aikata laifuka daban daban yayin da wasu kuma an kashe su yayin harin da aka kai. 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com



KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "COVID 19: An kama mutum 986 da suka saba dokar kulle a Kaduna"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?