--

Hana fita: Kungiyar AYCF ta caccaki Sanwo-Olu a kan watsi da yan Arewa wajen rabon tallafi

Hana fita: Kungiyar AYCF ta caccaki Sanwo-Olu a kan watsi da yan Arewa wajen rabon tallafi




- Kungiyar AYCF ta caccaki gwamnatin Lagas a kan rabon kayan rage radadin dokar hana fita a jahar


- Kungiyar ta hannun shugabanta na kasa, Yerima Shettima, ta ce an bar yan Arewa a Lagas a baya kwata-kwata wajen rabon kayan tallafin

- Shettima ya bayyana matakin gwamnatin jahar a matsayin rashin wayewa kuma ba mai karbuwa ba
Kungiyar matasan Arewa (AYCF) ta caccaki gwamnatin jahar Lagas a kan watsi da ta yi da al’ummanta a jahar wajen rabon kayan rage radadin hana fita.
A wata sanarwa da shugabanta na kasa, Alhaji Yerima Shettima ya aike wa Legit.ng, kungiyar ta ce tana sane da cewar an bar al’umman Lagas a baya kwata-kwata wajen rabon kayan tallafin.

Shettima ya bayyana cewa kungiyar na jin radadin halin bakin ciki da mutanenta ke ciki a jahar na watsi da aka yi da su.

Ya bayyana cewa kayan tallafin ba kyauta bane illa hakkin dukkanin mutane da ke jahar, ba tare da la’akari da yankin da suka fito ba a kasar


Shetimma ya kuma bayyana cewa hakan rashin wayewa ne, da rashin tunani kuma ba za a yarda gwamnatin Lagas ta yi watsi da yan Arewa ba a wannan lokaci da ake tsananin bukata.

A wani labarin kuma, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jahar Kaduna, ta caccaki Gwamna Nasir El-Rufai a kan tsawaita dokar hana fita na sa’o’i 24 da ya yi a jahar zuwa tsawon wani wata guda.


Jam’iyyar ta yi zargin cewa abun da ya fi damun gwamnatin jahar shine kudaden shiga da za ta samu daga tarar da wadanda suka saba dokar fitan za su biya.

PDP, yayin da ta ke caccakar tsarin yadda gwamnatin jahar ke bi wajen hana yaduwar annobar ta COVID-19, ta ce gwamnati mai mulki ba ta yi wa al’umma karin haske kan irin nasara da ake samu.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Hana fita: Kungiyar AYCF ta caccaki Sanwo-Olu a kan watsi da yan Arewa wajen rabon tallafi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?