--
Coronavirus: Jerin jihohin Najeriya da cutar ta bulla da adadin wadanda suka kamu a kowace jiha

Coronavirus: Jerin jihohin Najeriya da cutar ta bulla da adadin wadanda suka kamu a kowace jiha




Najeriya na ci gaba da samun hauhawan masu annobar coronavirus, inda a yanzu adadin masu ita ya kai 1,532 kamar yadda alkaluman hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar.


A daren ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, an samu karin mutane 195 da suka kamu, wanda shine mafi yawan adadi da aka samu a kasar cikin rana daya.

A wasu jerin rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter da misalin karfe 11:50 na dare, NCDC ta yi sanarwar yayin da masu coronavirus suka haura dubu daya a cikin kasa da watanni uku bayan an samu bullar cutar a kasar.
80 daga cikin masu cutar sun fito daga Lagas inda Kano ta zama ta biyu a alkaluman da mutane 38 –wadanda shine mafi yawa tun bayan barkewar cutar a jahar.
An salami mutane 255 bayan sun warke daga cutar yayin da 44 suka mutu, sannan har yanzu Lagas ce matattarar cutar a Najeriya.
A duniya gaba daya mutane 3,138,785 ne suka harbu da ccutar a fadin kasashe daban-daban.




 Amma ga rabe-raben masu COVID-19 a kowace jaha, kamar yadda ya ke a alkaluman NCDC yayin da cutar ke yaduwa a fadin jihohin kasar.


1. Lagos: 884
2. FCT: 158
3. Kano: 115
4. Ogun: 50
5. Gombe: 46

6. Osun: 34
7. Katsina: 30
8. Borno: 53

9. Edo: 30
10. Oyo: 21
11. Kaduna: 15
12. Bauchi: 29
13. Akwa Ibom: 12
14.Kwara: 11
15. Sokoto: 19
16. Ekiti: 8
17. Ondo: 8
18. Delta: 7
19 Rivers: 7
20. Taraba: 8
21. Enugu: 3
22. Niger: 2

23. Jigawa: 7
24. Abia: 2
25. Zamfara: 4
26. Benue: 1
27. Anambra: 1
28. Adamawa: 1
29. Plateau: 1
30. Imo: 1
31. Bayelsa: 1
32. Kebbi: 1
33. Ebonyi: 1
34. Nasarawa: 1


 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Coronavirus: Jerin jihohin Najeriya da cutar ta bulla da adadin wadanda suka kamu a kowace jiha"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?