--
Gwamnatin tarayya ta sake rage farashin litar man fetur a karo na biyu

Gwamnatin tarayya ta sake rage farashin litar man fetur a karo na biyu

Gwamnati tarayya ta sanar da sake farashin litar man fetur zuwa N123.50 kowacce lita daya. A wani jawabi da hukumar kula da farashin man fetur (PPPRA) ta fitar da yamacin ranar Talata, sakataren hukumar, Mista Abdulkadir Saidu, ya ce rsabon farashin litar man zai fara aiki ne daga ranar Laraba,
1 ga watan Afrilu, 2020. A cewar jawabin, "bisa dogaro da sabon tsarin duba farashin man fetur a gidajen mai kowanne wata,

mu na sanar da rage farashin litar man fetur zuwa N123.50. A ranar 19 ga watan Maris ne gwamnatin tarayya ta rage farashin litar man fetur daga N145 zuwa N125 sakamakon karyewar farashin danye man fetur a kasuwar duniya saboda annobar coronavirus. "Sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afrilu, 2020, kuma ya shafi dukkan gidajen man fetur da ke fadin Najeriya.

Jawabin ya kara da cewa, PPPRA da sauran hukumomin da suka dace za su dauki matakan tabbatar da cewa an yi wa sabon tsarin biyayya tare da yin kira ga jama da duk kamfanonin dillancin man fetur a kans su bawa gwamnati hadin kai wajen ganin sabon farashin ya fara aiki a kan lokacin da aka bayyan.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "Gwamnatin tarayya ta sake rage farashin litar man fetur a karo na biyu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?