LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Rundunar 'yan sanda ta kira Sheikh Jingir don sake amsa tambayoyi a kan saba dokar jiha

Rundunar 'yan sanda a jihar Filato ta kira shugaban majalisar koli ta malaman darikar Izalatil Bid'a Wa'ikamatis Sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, tare da yi masa tambayoyi an kan rashin biyayya ga umarnin jiha na hana dukkan wani taro har na addini a jihar saboda gujewa kamuwa da kwayar coronavirus.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya shaidawa manema labarai, da yammacin ranar Talata, cewa sun gayyaci Sheikh Jingir zuwa hedikwatar saboda ya jagoranci magoya bayansa sallar Juma'a duk da an saka dokar hana taron jama'a.

A cewar ASP Gabriel, kwamishinan 'yan sandan jihar, Isaac Akinmoyed, ya shaidawa Sheikh Jingir cewa rundunar 'yan sanda ba zata lamunci irin wannan halin ba a jihar. ASP Gabriel ya kara da cewa Sheikh Jingir, yayin da yake martani a gaban kwamishinan, ya dauki alkawarin yin biyayya ga dukkan umarnin gwamnatin jiha a kan yunkurin dakile annobar cutar covid-19.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1YKU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
b

Post a comment

0 Comments