--
Da dumi dumi: Babban basaraken jahar Kaduna ya rasu

Da dumi dumi: Babban basaraken jahar Kaduna ya rasu



Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, mun samu labarun rasuwar Alhaji Sa’ada Usman, Sarkin Jere na karamar hukumar Kagarko ta jahar Kaduna. Sarkin ya rasu ne bayan doguwar jinya da yayi fama da shi. Alhaji Sa’ad Usman shi ne mijin tsohuwar ministar kudi, kuma tsohuwar Sanatan Kaduna ta kudu, Sanata Nenadi Usman.

Wakilin watsa labaru na Jere, Ahmad D Yako ne ya bayyana haka a shafinsa na dandanin sadarwar zamani na Facebook, inda yace za’a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 2 na rana a fadar masarautar Jere. Da fatan Allah Ya jikan shi da gafara.

Sarkin Jere Source: Facebook Idan za'a tuna a shekarar 2014 ne wasu mutane suka kai ma Sarkin hari yayin da ya je yin sulhu tsakanin wasu bangarori biyu da basa ga maciji da juna a lokacin da wata rikici a kan fili ta taso a tsakaninsu. A dalilin wannan hari,

Sarkin ya samu munanan rauni a kansa, wanda hakan tasa aka garzaua da shi wani babban asibiti Cedar dake babban birnin tarayya Abuja a, daga bisani kuma aka mika shi zuwa asibitin kasar waje. Sai dai daga bisani rundunar Yansandan jahar Kaduna ta tabbatar da kama wasu daga cikin mutanen da suka kai ma Sarkin hari, kamar yadda kaakakin rundunar na wancan lokaci, Aminu Lawan ya bayyana.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "Da dumi dumi: Babban basaraken jahar Kaduna ya rasu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?