--
COVID-19: Wani mutum ya mutu a Kano bayan ya killace kansa

COVID-19: Wani mutum ya mutu a Kano bayan ya killace kansa

- Firgici da fargaba sun shiga zukatan jama'ar jihar Kano a kan mutuwar wani bawan Allah mazaunin kwatas din Gwammaja - Kamar yadda makwabtan Abdulrasheed Ibrahim suka bayyana, ya dawo kano ne daga Abuja a ranar Litinin da ta gabata

- Makwabtansa sun bayyana cewa sun ganshi yana wanke motarsa a ranar da ya dawo, kafin ya killace kansa Firgici da fargaba ta shiga zukatan jama'ar jihar Kano a kan mutuwar wani Abdulrasheed Ibrahim.

Mazaunin kwatas din Gwammajan ya mutu ne bayan ya killace kansa. Kamar yadda makwabtan mamacin suka bayyana, marigayi Abdulrasheed ya dawo Kano ne daga Abuja a ranar Litinin da ta gabata, jaridar The Nation ta ruwaito. Makwabtansa sun bayyana cewa sun ganshi yana wanke motarsa a ranar da ya dawo, kafin ya killace kansa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, mazaunan yankin sun dinga jin wani wari na fitowa daga gidan mamacin. Sun lura kuma yana cikin gida baya fitowa har na tsawon kwanaki uku.

Wadannan dalilan ne suka sa mazauna yankin suka sanar da 'yan uwanshi wadanda suka balle gidan tare da samunsa a mace. Kokarin zantawa da 'yan uwan mamacin ya gagara a halin yanzu. Daraktan cibiyar kula da lafiyar jama'a da hana yaduwar cutuka na jihar, Dr Imam Wada Bello, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu don jami'an kiwon lafiya sun isa wurin don daukar matakan da suka dace. Kamar yadda yace, an dau samfurin jinin mamacin kuma za a gwada. Ya tabbatar wa da jama'a cewa za a sanar musu sakamakon gwajin. A wani labari na daban,

cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta kammala kafa cibiyar gwajin cutar Coronavirus a asibitin koyarwar Malam Aminu Kano dake jihar Kano. Kafa wannan cibiyar cika alkawari ne da gwamnatin tarayya tayi na samar da dakin bincike na musamman domin gwajin cutar COVID-19 a Kano da wasu jihohin Arewa maso yamma.


KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19: Wani mutum ya mutu a Kano bayan ya killace kansa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?