\ Covi-19: Ansamar Da Cibiyar gwajin coronavirus a jihar kano - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Covi-19: Ansamar Da Cibiyar gwajin coronavirus a jihar kano - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
 • LABARAN YAU

  Friday, April 10, 2020

  Covi-19: Ansamar Da Cibiyar gwajin coronavirus a jihar kano

  Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta kammala kafa cibiyar gwajin cutar Coronavirus a asibitin koyarwar Malam Aminu Kano dake jihar Kano, ta farko a Arewa

  Kafa wannan cibiyar cika alkawari ne da gwamnatin tarayya tayi na samar da dakin bincike na musamman domin gwajin cutar COVID-19 a Kano da wasu jihohin Arewa maso yamma.

  Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, wanda ya kai ziyarar ganin ido cibiyar a daren Alhamis ya bayyana cewa daga yanzu za a fara gwaji a Kano.

  Yace: “Daga yanzu, ba za a sake kai samfurin jinin mutane Abuja ba domin gwaji. A Kano za a yi.“

  “Mun zo yawon ganin ido domin tabbatar da abinda ke kasa ne, kuma bisa abinda muka gani a cikin dakin gwajin, an kammala shirya kayayyakin kuma an fara gwaji.“
  Ya mika godiyar gwamnatin jihar Kano karkashin gwaman Abdullahi Umar Ganduje, ga gwamnatin tarayya bisa wannan cibiya a Kano.

  Gawuna ya ce sauran jihohi masu makwabtaka da Kano za su iya zuwa gwaji cibiyar.

  Yayinda suke zagaye cikin cibiya, wani maaikacin NCDC, AbdulMaid Musa, ya ce babu irin gwain da ba za a iya ba a cibiyar.

  Hakazalika an fara horar da maaikatan asibitin AKTH da gwamnatin jihar kan yadda zasu rika amfani da kayayyakin.

  Shugaban asibitin AKTH, Farfesa Abdurrahaman Sheshe, ya yabawa jajircewan kwamitin yakar Coronavirus ta jihar karkashin jagorancin mataimakin gwamnan bisa yaddaaka wayar da kan mutane kan matakan takaita yaduwar cutar.

  Gabanin kafa wannan cibiya, babu wajen gwajin cutar Coronavirus ko daya a jihohin Arewacn Najeriya 19.

  Birnin tarayya Abuja ake kai samfurin mutanen Arewa sannan a dawo da sakamakon.

  Kano ta shiga sawun jihohi irinsu Legas, Edo, Osun, Oyo, da Abuja masu cibiyar gwajin cutar.KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


  LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 


  Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

  KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
  https://www.appcreator24.com/app757657
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Covi-19: Ansamar Da Cibiyar gwajin coronavirus a jihar kano Rating: 5 Reviewed By: Admin