--
Ba shiga, ba fita: An rufe Daura bayan an tabbatar da samun mutane 3 da cutar covid-19

Ba shiga, ba fita: An rufe Daura bayan an tabbatar da samun mutane 3 da cutar covid-19



Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da umarnin rufe karamar hukumar Daura; ba shiga, ba fita, bayan an tabbatar da samun mutane uku da suke dauke da kwayar cutar covid-19.

Sanarwar rufe jihar ta fito ne a yau, Juma'a, kamar yadda jaridu da dama a fadin kasa suka wallafa. Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ne ya bayar da umarnin rufe karamar hukumar bayan an tabbatar da bullar annobar covid-19 a yankin. Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, dan asalin karamar hukumar Daura ne.

A jerin wasu sakonni da aka wallafa a shafin Tuwita, Masari ya ce an tabbatar da samun kwayar cutar covid-19 a jikin mata da 'ya'yan likitan da kwayar cutar covid-19 ta kashe a Katsina a cikin satin nan. Masari ya bayyana cewa an tura jinin mutane 23 domin gudanar da gwaji a kansu bayan mutuwar likitan, kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa matarsa da 'ya'yansa sun kamu da kwayar cutar.

Gwamnan ya ce, gwamnati za ta bayar da tallafi ga mazauna karamar hukumar na tsawon lokacin da dokar za ta cigaba da aiki.

"Za mu cigaba da sa ido da bibiyar al'amura. Ba za mu yi kasa a gwuiwa ba wajen saka dokar rufe duk wata karamar hukuma da aka tabbatar da samun bullar annobar covid-19 ba. Ita kanta jihar za mu iya rufeta gaba daya idan yanayi ya nuna akwai bukatar yin hakan. "Za mu bar shagunan sayen magani da na kayan abinci guda uku, wadanda jama'a za su ke sayen kaya a wurinsu bisa sa idon hukuma domin tabbatar da biyayya ga matakan kare kai da dakile yaduwar cutar," a cewar Masari.


KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaappπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ba shiga, ba fita: An rufe Daura bayan an tabbatar da samun mutane 3 da cutar covid-19 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?