--
Coronavirus: Ana bincike kan mutum 25 a Kano

Coronavirus: Ana bincike kan mutum 25 a Kano



Gwamnatin Jihar kano ta ce tana gudanar da bincike kan mutum 25 da ake zargin suna dauke da cutar coronavirus a jihar.

A wani taron manema labarai a ranar Alhamis a Kano, Kwamishinan Lafiyar Jihar, Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce tuni gwaji ya nuna 22 daga cikinsu ba sa dauke da cutar yayin da ake jiran sakamakon gwaji na mutum uku.

Ya kara da cewa mafi yawan rahotannin da suke samu daga mutane, jita-jita ce, sannan ya ce sun samar da wasu lambobi na kira domin bayar da rahotannin wadanda ake tunanin sun kamu da coronavirus.
Kazalika Aminu Ibrahim ya ce Alhaji Aliko Dangote zai gina cibiyar kebe masu coronavirus mai gado 500, sabanin 600 da wasu kafofin yada labarai suka rawaito.

Kwamishinan ya kuma jaddada kokarin gwamnatin Kano na ci gaba da sanya ido kan dokar hana shiga jihar da suka kafa tun a makon da ya gabata.

Makociyarta wato Jihar Kaduna, dokar hana fita baki daya aka saka duk da cewa gwamnati ta sassauta a ranar Laraba.


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Coronavirus: Ana bincike kan mutum 25 a Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?