--
An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili

An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili

An kashe wani kansilar karamar hukuma a jihar Anambra, Chukwuebuka Ikeji a kan rikicin fili. Sakamakon hakan, fusatattun matasa a unguwar sun hada kai sun kone gidan Emmanuel Ukandu wanda ake zargi da kashe kansilar. Har wa yau,

matasan sun kuma kona motar bus mallakar Emmanuel Ukandu da ake zargin da ita ya kashe kansilar. Lamarin ya faru ne a garin Umunna, Umuchukwu a karamar hukumar Orumba ta Kudu na jihar ta Anambra.

An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili Source: UGC 

An gano cewa Ukandu wanda suka samu rashin jituwa da mammacin saboda fili ya yi amfani da motarsa ne ya nike shi duk da gargadin da yaron motarsa ya masa kan afkuwar hakan.

Mai magana da yawun rundunar tsaro ta NSCDC a jihar, Edwin Okadigbo ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin. Ya ce an sanar da ofishin NSCDC na Orumba ta Kudu afuwar lamarin a ranar Laraba. Okadigbo ya ce, "Binciken da muka gudanar kawo yanzu ya nuna cewa wanda ake zargin ya dade yana rikici da mutane kan mallakin wata fili kuma yana jin haushin duk wadanda ba su goyon bayansa.

"Garin haka ne ya kashe mammacin wanda shine kansila mai wakiltan Umuchukwu a karamar hukumar Orumba ta Kudu, har yaron motarsa ma ya yi ta faษ—a masa cewa idan bai dakatar da motarsa ba zai buge mutumin."
LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?