--
Zan bi masu zabe har gida ina daka musu sakwara har sai naci zabe- Dan takara

Zan bi masu zabe har gida ina daka musu sakwara har sai naci zabe- Dan takara

- Dan takarar kujerar majalisa mai wakiltar Wuogon na Yamma, John Dumelo ya bayyana cewa ba zai daina yakin neman zabe na gida-gida ba har sai ya ci zaben 

- Bayan dan wasan kuma mai jinkan mutanen ya wallafa hotunan shi yana dakawa jama'a sakwara a shafinshi na twitter, ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamanin sunyi caa a kanshi

 - Amma kuma, John Dumelo ya bada amsar cewa jajircewa da aiki tukuru ne ke bada tabbacin zai yi nasara a zaben don haka ba zai daina wannan salon yakin neman zaben ba Dan takarar kujerar majalisa mai wakiltar Wuogon na Yamma, 

John Dumelo ya bayyana cewa ba zai daina yakin neman zabe na gida-gida ba har sai ya ci zaben. Bayan dan wasan kuma mai jinkan mutanen ya wallafa hotunan shi yana dakawa jama'a sakwara a shafinshi na twitter, ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamanin sunyi caa a kanshi. Sun ce daka sakwara, yin kitso da kuma taya masu zabe aiyukan gida ba zai zama tabbacin cewa za a zabeshi ba,

Amma kuma, John Dumelo ya bada amsar cewa jajircewa da aiki tukuru ne ka bada tabbacin zai yi nasara a zaben don haka ba zai daina wannan salon yakin neman zaben ba. Kamar yadda yace, zai yi komai da dan Adam zai iya yi don ganin ya samu nasara koda kuwa zai dinga daka wa jama'a sakwara ne. Akwai abin mamaki idan aka ji dan siyasa na fadin hakan, amma dai zamu kalmashe kafa mu ga abinda gobe za ta haifar. LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Zan bi masu zabe har gida ina daka musu sakwara har sai naci zabe- Dan takara"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?