--
Za a hana amfani da injin janareto a Najeriya baki daya - Majalisar dattawa

Za a hana amfani da injin janareto a Najeriya baki daya - Majalisar dattawa

- Majalisar dattawa ta gabatar da kudurin da zai hana amfani da injin janareto a Najeriya

- Majalisar dai a yau Larabar nan tayi zama na farko akan wannan kuduri, inda idan har ta aminta dashi hakan zai kawo karshen amfani da injin janaretor a fadin Najeriyan

A yau Laraba ne 11 ga watan Maris, majalisar dattawan Najeriya ta gabatar da kudurin da zai hana amfani da injin janareto a Najeriya baki daya.

Kudurin wanda Sanata Bima Muhammadu Emagi, dan majalisa mai wakiltar jihar Neja ta kudu a karkashin jam'iyyar APC, shine ya gabatar da kudurin wanda aka yi zama a kanshi karo na farko a dakin majalisar.


Idan har aka sanya hannu akan dokar, to hakan shine zai kawo karshen amfani da injin janareto a Najeriya baki daya.

To sai dai kuma har yanzu matsalar wutar lantarkin a Najeriya ta zama gado tun iyaye da kakanni har yanzu babu wani canji.


Rashin wutar lantarki tana daya daga cikin babban kalubalen da 'yan Najeriya suke fuskanta shekaru masu yawan gaske.

Wannan dai na zuwa ne yayin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta nuna cewa tana yin iya bakin kokarinta wajen ganin ta dai-daita lamarin na wutar lantarki a fadin kasar ta Najeriya.


A wani bangaren kuma ana ta faman tataburza a Najeriyan sanadiyyar sauke Sarkin Kano da gwamnatin jihar Kano ta yi a jiya sanadiyyar yiwa gwamnatin rashin da'a kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.


Mutane dai kowa na fadin albarkacin bakinsa sanadiyyar wannan lamari na bazata wanda babu wanda ya taba tunanin hakan za ta faru.

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Za a hana amfani da injin janareto a Najeriya baki daya - Majalisar dattawa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?