--
Tunbuke Sanusi II da aka yi ya fusata Attajirin Najeriya, ya rubutawa CBN wasika

Tunbuke Sanusi II da aka yi ya fusata Attajirin Najeriya, ya rubutawa CBN wasika

Shugaban kamfanin ANAP Business Jets Limited, Mista Atedo Peterside, ya yi watsi da wani tayi da babban bankin Najeriya ya yi masa na zaman tattaunawa.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya kira wani taro da za a zauna da Masana da manyan ‘yan kasuwa da duk wadanda ke da ilmin harkar tattali a kan tebur.

Atedo Peterside ya nuna cewa ba zai halarci wannan taro ba. Yanzu haka dai ba ya Najeriya inda ya ke wajen wani babban taro na Masana aikin banki a ketare.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, kasashen da Birtaniya ta raina su na wani taro ne a Yankin Westminster Abbey da ke Birnin Landan.

Takaicin samun labarin manyan abubuwan da su ke faruwa yanzu na tunbuke Sarkin Kano daga ofis ne ya hana Peterside karbar wannan gayyata na bankin CBN.

Haka zalika shugaban bankin IBTC ya yi bakin ciki da jin jawabi cewa za ayi wa tsohon Sarkin na Kano daurin talala yayin da ya ke zaman gudun hijira a wani Kauye.

“Na zabi in kauracewa wannan taro na ku ne domin in yi amfani da wannan dama in jawo hankalin sauran jama’a game da takaici na abubuwan da su ka faru.”

Wasikar ta ce: “Ku yi hakuri, ku gafarce ni, a halin yanzu ba ni da sha’awar fakewa kamar abubuwa su na tafiya daidai har in cigaba da ayyukan da ke gaba na.”

Sai dai Mista Peterside, ya bayyana cewa nan gaba kadan zai tuntubi CBN tare da ba ta shawarwarin yadda za ta magance matsalar tsilla-tsillar tsare-tsarenta.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Tunbuke Sanusi II da aka yi ya fusata Attajirin Najeriya, ya rubutawa CBN wasika"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?