MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"

Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Thursday, March 26, 2020

  Yanzu-yanzu: Mutum 1 na kusa da gwamnan Bauchi sun kamu da cutar Coronavirus

  Mutum daya ya sake kamuwa da cutar Coronavirus a Bauchin Yakubu. Kwamishanan kiwon lafiyan jihar, Dakta Aliyu Maigoro, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.

  Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa mutane 48 da suka hadu da gwamna Bala Abdulkadir sun killace kansu. An wajabta musu killace kansu na tsawon kwanaki 14 ne domin sanin ko sun kamu da cutar. Kwamishanan yace daga cikin mutane 48 a akayiwa gwaji, sakamakon 38 ya fito kuma daya kadai ya kamu. Ya ce wanda ya kamu dan shekara 62 ne. 

  Maigoro ya yi kira ga masu hannu da shuni a jihar su taimakawa gwamnati wajen dakile cutar. Yace: "Muna kira ga masu hannu da shuni da kuma abokan arziki su taimakawa jihar wajen dakile wannan cuta da kayayyakin aiki da magunguna." 

  A karshe, Maigoro ya ce gwamnatin jihar ta zabi Asibitin Bayara matsayin daya daga cikin wuraren da za'a yi jinyar wadanda suka kamu da cutar. Za ku tuna cewa gwamnan jihar, Bala AbdulKadir Mohammed, ya kamu da cutar bayan zama cikin jirgi tare da dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Mohammed Atiku Abubakar, ya fara kasuwa. 

  Hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya wato NCDC, ta bayyana cewa an sake samun karin mutane goma sha hudu da suka kamu da cutar coronavirus a kasar. A wani jawabi da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris da daddare, hukumar ta ce mutane 12 daga cikinsu a Lagos suke yayin da sauran biyu kuma suke Abuja. LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Yanzu-yanzu: Mutum 1 na kusa da gwamnan Bauchi sun kamu da cutar Coronavirus Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI