--
YANZU-YANZU: Ganduje ya kwancewa Sarkin Kano rawani

YANZU-YANZU: Ganduje ya kwancewa Sarkin Kano rawani

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu. Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020. Yace: "Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da tsige sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II."

YANZU-YANZU: Ganduje ya kwancewa Sarkin Kano rawani Source: Twitter 

Mun kawo muku rahoton cewa Mambobin majalisar dokokin jihar Kano sun barke da fada da safen nan yayinda kwamitin binciken sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ke shirin gabatar da rahoton kwance masa rawani. Daily Nigerian ta ruwaito. Rikicin ya fara ne yayinda mataimakin kakakin majalisar, Hamisu Chidari, 

ya nemi izinin gabatar da rahoton yau. Amma yan majalisar jam'iyyar adawa ta PDP suka ce a dakatad da gabatar da rahoton binciken sai ranar Talata domin kara dubi cikin rahoton; kawai sai rikici ya barke wanda ya kai ga dan majalisa mai wakiltar Warawa ya dauke sandar majalisa. 

Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa akwai alamun cewa yau za'a kwancewa sarki Sanusi rawani ko ta rahoton majalisar, ko kuma ta hukumar yaki da rashawar jihar. 



LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "YANZU-YANZU: Ganduje ya kwancewa Sarkin Kano rawani "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?