--
Nan ba da dadewa ba zamu nada sabon sarki - Ganduje

Nan ba da dadewa ba zamu nada sabon sarki - Ganduje

Bayan sauke Muhammadu Sanusi II a daga saurautar sarkin Kano, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga al'ummar jihar su kwantar da hakunlansu kuma za'a nada sabon sarki nan ba da dadewa ba. Sakataren yada labaran gwamna Ganduje, Abba Anwar, yace: "Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga al'umma sun kasance masu bin doka kuma su kwantar da hankulansu. 

Za'a nada sabon sarkin Kano ba da dadewa ba." Mun kawo muku rahoton cewa gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu. Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020. Yace: "Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da tsige sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II." Hakazalika, sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya saki jawabi kan dalilin da yasa gwamnatin jihar ta tunbuke sarkin Kano daga kujerarsa.


Ya ce an kwancewa Sanusi Lamido Sanusi rawani ne saboda yan zubar da mutunci da kuma ko oho da dokokin masarautar. Baya ga haka, Usman Alhaji ya ce Sarkin ya daina halartan dukkan ganawa da gwamnatin jihar ta shirya ba tare da wani uzuri kwakkwara ba kuma hakan rashin biyayya ne ga gwamnati. 

Yace: "Ya kamata a sani cewa a lokuta da dama, Malam Muhammadu Sanusi II ya kasance mai karya sashe na 3 na dokar masarautar kuma idan aka cigaba da zuba masa ido, zai lalata mutuncin masarautar." "An tunbukeshi ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar" LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Nan ba da dadewa ba zamu nada sabon sarki - Ganduje"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?