Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Monday, March 9, 2020

  Da duminsa: Yau Ganduje zai nada sabon Sarkin Kano - Majiya

  Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, zai nada sabon sarkin Kano yau bayan kwancewa Muhammadu Sanusi na biyu rawani. Majiya mai siqa ta tabbatar mana cewa gwamnan zai sanar da sabon sarkin kafin karfe 5 na yamma. 

  A cewar wani jami'in tsaro dake cikin dakin ganawar da aka tunbuke Sanusi, ya ce yau za'a nada sabon sarki. Hakazalika kwamishanan yada labaran jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya tabbatar DT cewa yau za'a sanar da sabon sarki. Yace: "Yau za'a alanta sabon sarki, saboda gwamna na shirin sanar da sunansa na da awa daya." Mun kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga al'ummar jihar su kwantar da hakunlansu kuma za'a nada sabon sarki nan ba da dadewa ba.

  Sakataren yada labaran gwamna Ganduje, Abba Anwar, yace: "Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga al'umma sun kasance masu bin doka kuma su kwantar da hankulansu. Za'a nada sabon sarkin Kano ba da dadewa ba." Gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu. 

  Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020. Yace: "Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da tsige sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II." Hakazalika, sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya saki jawabi kan dalilin da yasa gwamnatin jihar ta tunbuke sarkin Kano daga kujerarsa. Ya ce an kwancewa Sanusi Lamido Sanusi rawani ne saboda yan zubar da mutunci da kuma ko oho da dokokin masarautar.


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Da duminsa: Yau Ganduje zai nada sabon Sarkin Kano - Majiya Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI