MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"
 • Latest News

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Monday, March 9, 2020

  Yanzun-nan: An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya

  - An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya - Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya sanar da hakan ta hannun hukumar kula da yaduwar cututtuka na Najeriya (NCDC) - Mutum na biyu da ke dauke da cutar ya kasance cikin wadanda aka killace sakamakon hulda da dan kasar Italiya da ya shigo da cutar Najeriya 

  Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya sanar da samun wani mutum na biyu da ke dauke da cutar coronavirus a Najeriya. Jaridar Punch ta ruwaito cewa mutumin ya yi hulda da dan kasar Italiya da ya shigo da cutar coronavirus Najeriya.

  Yanzun-nan: An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya Source: Twitter An tattaro cewa mutumin ya kasance daya daga cikin wadanda aka killace. Cibiyar kula da yaduwar cututtuka na Najeriya (NCDC) ce ta tabbatar da hakan a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin, 9 ga watan Maris.    An gano mai dauke da cutar ne a jihar Ogun cikin mutanen da aka kebance tun tuni, kuma an gano cutar a jikinsa ne a kokarin da muke na gano duk wadanda suka yi alaka da mai dauke da cutar na farko dan kasar italiya." A wani lamari makamancin haka mun ji cewa cikin matakan da take dauke wajen takaita yaduwar cutar Coronavirus, 

  Kasar Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantu da jami'o'in masarautar fari daga ranar Litinin har ila ma sha'a llahu. Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA ta sanar da cewa ma'aikatar Ilimin kasar ta sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Febrairu 2020. 

  Jawabin yace: "An yanke shawarar kulle dukkan makarantu ne saboda kyakkyawar soyayyar da shugabancin ke yiwa yaranta kan tsaronsu kuma za'a samar da wasu hanyoyin ilmantar da su daga gidajensu." Ministan harkokin ilimin Saudiyya ya bada umurnin ilmantar da yara daga gidajensu ta hanyar na'urorin zamani. Kawo yanzu, mutane 11 sun kamu da cutar a kasar ta Saudiyya.
  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Yanzun-nan: An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI