MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"

Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Monday, March 16, 2020

  Toh fa! Likitan Najeriya ya mutu a sanadiyyar cutar Coronavirus


  Karamin ministan harkokin kiwon lafiya, Adeleke Mamora ya bayyana cewa an samu wani likita dan Najeriya da ya rasa ransa a sakamakon annobar cutar Coronavirus a kasar Canada. Daily Nigerian ta ruwaito Minista Mamora ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake bayar da jawabi a kan cutar Coronavirus ga manema labaru inda yace sunan wannan likita dan Najeriya Olumide Okunug


  “Ya kamata kowa ya zama mai lura da ankara, na ji jama’a na cewa wai bakar fata na da kariya daga cutar Coronavirus, wai ba za ta iya cutar damu ba, don haka nake shaida mana cewa bakar fata kuma dan Najeriya ya mutu a sanadiyyar cutar. “Mun samu labarin wani likita dan Najeriya dake zama a kasar Italiya wanda ya mutu a sakamakon cutar, don haka akwai bukatar mu yi taka tsantsan game da sauraron batutuwan da basu tabbata ba.” Inji shi. 

  Rahotanni sun bayyana cewa Dakta Okunugu dan shekara 63 ya kamu da cutar ne yayin wata ziyara daya kai kasar Canada. A wani labarin kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Ondo ta bayyana cewa tana gudanar da binciken kwakaf bisa wani mummunan lamari daya faru a jahar inda wani Dansanda ya halaka kan sa bayan ya kashe matarsa. Dansandan mai suna Sajan Saliu Tolulope ya dirka ma matarsa bindiga ne, 

  sa’annan ya bindige kansa har lahira a makon da ta gabata a unguwar Akungba-Akoko na karamar hukumar Akoko ta Yamma a jahar Ondo. Lamarin ya faru ne a gaban yaran mamatan biyu, inda babban yake dan shekara 2, karamin kuma bai wuce watanni uku da haihuwa ba. Makwabtan su sun tabbatar da cewa sun ji yo muryar ma’auratan suna cacar baki, daga nan sai kawai suka ji karar harbin bindiga, koda suka garzaya gidan sai dai gawarsu kawai suka tarar. 

  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Toh fa! Likitan Najeriya ya mutu a sanadiyyar cutar Coronavirus Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI