Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Tuesday, March 10, 2020

  Sunusi ya baiwa Ganduje sa’o’i 24 ya sake shi, ko kuma ya dauki mataki a kansa

  Korarren sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya dauki alwashin shigar da gwamnatin jahar Kano gaban kotu biyo bayan tsige shi da ya yi daga mukamin Sarautar Kano, tare da garkame shi. Lauyan Sanusi, Abubakar Mahmoud SAN ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, inda yace Sunusi ya basu umarnin kalubalantar tsige shi da aka yi, da kuma garkame shi da aka yi. 

  A cewar Mahmoud, garkame Sarki a wani wuri tare da hana shi walwala ba shi da asali a kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ya yi kira ga gwamnatin Kano ta sakan masa mara ya yi fitsari cikin sa’o’I 24 ko kuma ya kai shi kotu. 

  “Sakamakon umarnin tsohon Sarki ta hannun babban hadiminsa, ya bamu daman shigar da karar gwamnati gaban kotu domin kalubalantar tsige garkame shi tare da fatattakarsa daga garin Kano, muna da tabbacin hakan ya saba ma sashi na 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya daya baiwa kowa daman walwala.

  “Mun sanar da kwamshinan Yansanda haramcin takura ma Sarki tare da garkame shi da kuma hana shi walwala, hatta kais hi jahar Nassarawa ba tare da son ran shi ba, Sarkin ya shaida ma kwamishinan Yansanda cewa abokansa sun shirya masa jirgi da zai dauke shi tare da iyalansa zuwa Legas, 

  don haka ya nemi a basu tsaro har zuwa filin sauka da tashin jirage don su yi tafiyarsu. “Amma kwamshinan ya ki, saboda a cewarsa wannan ba shi bane umarnin da aka bashi, kwamishinan yace sun yarda iyalan Sarkin su tafi Legas, amma Sarki ya bi su su tafi Abuja, daga nan su kai shi Nassarawa. Ta tabbata jami’an tsaro a shirye suke su tilast Sarkin, don haka muka biye musu. 

  “Mun raka gwamnan har zuwa sansanin rundunar Sojan sama dake Kano inda aka dauki Sarkin a wani jirgi da misalin karfe 6:40 na dare, daga nan iyalansa kuma suka bi jirgin da abokansa suka shirya masa suka tafi Legas. “Wannan dokar sallamar sarki mai murabus daga gari ya samo asali ne a zamanin mulkin turawa na mulkin mallaka, amma ba shi da tushe a kundin tsarin mulkin Najeriya.

  Don haka muka yi mamakin yadda hakan ya cigaba da aiki a wannan zamani.” Inji shi. Daga karshe Mahmoud ya yi kira ga yan Najeriya da kasashen duniya su sa baki don tabbatar da an saki Muhammadu Sunusi don kare raywarsa da tabbatar da yancinsa. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Sunusi ya baiwa Ganduje sa’o’i 24 ya sake shi, ko kuma ya dauki mataki a kansa Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI