--
"Daurin talalar da aka yi wa Muhammadu Sanusi II ya ci karo da doka da hakkin ‘Dan Adam" |Amnesty International

"Daurin talalar da aka yi wa Muhammadu Sanusi II ya ci karo da doka da hakkin ‘Dan Adam" |Amnesty International

Kungiyoyi masu rajin kare hakki da nemawa Bil Adama ‘yanci sun fara magana game da gudun hijirar da aka tura tsohon Sarkin Birnin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II. 

Wadannan kungiyoyi sun bayyana cewa tsare tsohon Sarkin da aka yi a wani Kauye a jihar Nasarawa ya sabawa dokokin Najeriya, sannan kuma an keta masa hakkinsa.

Kungiyar Amnesty International ta na cikin ‘yan gaba-gaba wajen wannan kira. Darektan kungiyar a Najeriya, Osai Ojigho ya fitar da jawabi na musamman a Ranar Talata. 

Osai Ojigho ya bukaci hukumomin Najeriya su saki tsohon Mai martaba Muhammadu Sanusi II. A cewarsu, tsare shi da hana sa magana ya ci karo da dokokin gida da kuma na waje. 

Haka zalika kungiyoyi irinsu CISLAC sun nuna damuwarsu game da yadda ake ta tsare tsohon Sarkin Birnin bayan an tube masa rawanin gidan dabo a cikin farkon makon nan. 



 Darektan kungiyar CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya bayyana cewa maida tsohon Sarkin zuwa Nasarawa da karfi da yaji ya ci karo da sashe na 34, 35, 36, 40 da 41 na tsarin mulki. 

Shugaban kungiyar nan ta Concerned Nigerians, Deji Adeyanju, ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran hukumomi wasika game da tsare tsohon Sarkin. A takardar da Deji Adeyanju ya aikawa Jami’an tsaron Najeriya da ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Abuja, 

ya ce tura Sanusi II gudun hijira ya sabawa doka da tsarin mulkin kasa. SERAP ta ja hankalin majalisar dinkin Duniya game da halin da tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya ya ke ciki. Alamu na nuna cewa za a kai kara kotu idan ba a sake shi ba. 



LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to ""Daurin talalar da aka yi wa Muhammadu Sanusi II ya ci karo da doka da hakkin ‘Dan Adam" |Amnesty International"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?