MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"

Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Wednesday, March 11, 2020

  Shekau ya mayar da martani bayan saka kyautar $7m ga duk wanda ya kama shi (Bidiyo)

  Shugaban kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau yayi martani a kan kyautar da hukumar jami'an farin kaya ta Amurka ta saka ga duk wanda ke da bayanai a kansa wadanda zasu bada damar kama shi. Hukumar jami'an tsaron ta fararen kayan ta kasar Amurka, 

  ta bada wannan sanarwan ne a ranar 5 ga watan Maris na 2020. Bassim-AMG, ma'aikacin yada labarai da ya kware a kawo rahotanni a kan ta'addanci ne ya wallafa bidiyon shugaban 'yan ta'addan yana martani a kan kyautar dala miliyan bakwai din da aka saka a kanshi.

  Kamar yadda dan jaridar ya sanar, a bidiyo mai mintoci 26 da Shekau ya saki, ya kara jaddada cewa Amurka, Isra'ila da Najeriya duk kasashen kafirai ne kuma Amurka ce hedkwatar rashawa. Shugaban 'yan ta'addan yace Amurka na yakar Musulunci ta duk yadda ba a tsammani. 

  Ya kara da bukatar sanin dalilin da za ta saka naira biliyan 2.5 ko dala miliyan bakwai duk don a kama shi. Shekau ya kara da ikirarin cewa Amurka ba za ta taba gano inda yake ba, ballantana ta kama shi. Ya ce kwata-kwata baya tsoron su kama shi don shi ba kafiri bane. Ya yi farin ciki tare da nuna nishadin wannan kudi da aka saka don nemo shi ta hanyar harba harsasai masu yawa a sararin samaniya.


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Shekau ya mayar da martani bayan saka kyautar $7m ga duk wanda ya kama shi (Bidiyo) Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI