Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Wednesday, March 11, 2020

  Sautin murya: Abinda Sheikh Dahiru Bauchi ya fada a kan tube rawanin Sanusi II  A yayin da jama'a ke cigaba da bayyana mabanbantan ra'ayoyi a kan tsige Muahammadu Sanusi II daga kujerar sarkin Kano, babban malamin darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya tofa albarkacin bakinsa.

  A wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na radiyon BBC, Sheikh Dahiru Bauchi, ya ce tun bayan samun sanarwar tube Sanusi II, suke aika sako ga magoya bayansu a kan su kwantar da hankalinsu, kar su tashi hankalinsu a kan abinda ya faru.

  A cewar, babban malamin, wuta da kudi suna hannun gwamnta, a saboda haka zasu iya daukan mataki marar dadi a kan wadanda suka fito domin nuna rashin jin dadinsu.

  Sheikh Dahiru Bauchi ya yi addu'a ga tsohon Sarki Sanusi tare da yi masa fatan alheri a rayuwa.

  "Su suke da wuta a hannusu, su suke da kudi a hannunsu, zasu iya bayar da umarnin a harbe mutane. Babu gwamnati a hannunmu, a saboda haka babu wanda zai saurare mu," a cewar Sheikh Dahiru.

  Sannan ya cigaba da cewa, "a kwantar da hankali, kar a tayar da hankali, a cigaba da addu'a, gara a yi shiru, Allah zai yi mana sakayya."

  Saurari Sautin Muryar Shehin Malamin AnanπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Sautin murya: Abinda Sheikh Dahiru Bauchi ya fada a kan tube rawanin Sanusi II Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI