Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Wednesday, March 11, 2020

  Buhari ne ya bayar da umarnin tumbuke Sarkin Kano – Kwankwaso


  Tsohon gwamnan jahar Kano, kuma wanda ya nada tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa tubuke rawanin Sarkin Kano umarni ne daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari. BBC ta ruwaito Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da ya yi da ita game da batun tsige tsohon Sarkin na Kano, inda ya bayyana hakan a matsayin abin bakin ciki ga jahar Kano, Najeriya da ma duniya gaba daya. 

  A cewar Kwankwaso: "Shuwagabannin gwamnatin Kano da kansu ne su ke cewa umarni aka ba su, kuma shi ya ba su umarni….Shugaba Buhari yana tsoma hannu cikin al'amuran jihar Kano, Inda ya kamata ya sa hannun sai mu ga ba nan ya sa hannu ba, inda kuma bai kamata ya sa hannu ba, sai mu ga a nan ya sa hannu….sai dai musamman mu nan a Kano yadda muke gani yana hargitsa inda yake sa hannu". 

  Haka zalika Kwankwaso ya musanta zargin da ake yadawa na cewa wai tun yana gwamna ya taba baiwa tsohon Sarkin takardar gargadi har sau uku sakamakon irin furucin da yake furtawa, inda yace; “Ni ban taba ba Mai martaba sarki wata takardar gargadi ko ma wani abu irin wannan ba". 

  Game da zargin da ake masa tare da magoya bayansa yan Kwankwasiyya game da rura rikicin dake tsakanin Gwamna Ganduje da tsohon Sarkin Kano kuwa, Kwankwaso ya ce su a kullum suna bayan mai gaskiya ne. Sa’annan ya bayyana cewa babban abin da yasa sarkin ya gamu da fushin Gwamna Ganduje bai wuce bukatar da ya bayyana ba na cewa a baiwa duk wanda ya ci zaben gwamnan Kano nasararsa. A wani labari kuma, wani matashi mai ji da kardi daga jahar Jigawa ya kaddamar da tattaki zuwa jahar Kano domin taya sabon Sarkin Kano, mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero murnar darewar karagar mulki. 


  Rahotanni sun bayyana cewa wannan matashi mai suna Umar dan asalin jahar Kano ne, amma yana karatu a jami'ar gwamnatin tarayya dake birnin Dutse na jahar Jigawa. Murna da farin ciki da ya turnuke Umar biyo bayan sanar da Aminu Ado a matsayin sabon Sarkin Kano ne yasa ya fara wannan tattaki domin yin jinjinar ban girma, tare da bayyana ma sabon sarkin farin cikinsa da kuma fatan alheri. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Buhari ne ya bayar da umarnin tumbuke Sarkin Kano – Kwankwaso Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI