Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Tuesday, March 10, 2020

  Sarkin maroka: Mabaracin da ya mallaki gidaje biyar, motoci 20 da kamfanin ruwan leda

  - Alhaji Umar Dikko ba mabaraci bane kamar mabaratan da akae gani a kan tituna nr wadanda ke neman sadaka - Duk da yana da nakasa, Alhaji Umar na da tarin dukiya kuma yana da mata hudu ne da yara 18

  - Shi ne sarkin Maroka na yankin Ajegunle da ke jihar Legas amma kuma ya kafa tarihi Alhaji Umar Dikko ba mabaraci bane kamar mabaratan da ake gani a kan tituna wadanda ke neman sadaka daga hannun masu tausaya musu. Alhaji Umar Dikko dai mabaraci ne amma yana da babban banbanci da sauran mabarata. 

  Shi ne sarkin Maroka na yankin Ajegunle da ke jihar Legas, amma kuma ya kafa tarihin zama mabaracin da ya fi kowanne arziki a Najeriya. Duk da yana da nakasa, Alhaji Umar na da tarin dukiya kuma yana da mata hudu ne da yara 18. Yana kasuwancin sufuri ne kuma ya mallaki kamfanin yin ruwan leda. Yana da gidaje ginannu guda biyar a jihar Kano.

  A yayin da yake labarta yadda ya nakasa, Alhaji Umar Dikko ya ce, hakan ta faru da shi ne tun yana da shekaru uku kacal a duniya. Ya saba yawo a titunan don samun abinda zai ciyar da kan shi don iyayen shi sun sake shi. “Na rasa kafa ne lokacin da nake da shekaru uku sakamakon cutar polio. 

  Iyayena da sauran ‘yan uwana basu damu da ni ba balle su kula dani. Mahaifiyata ce take kokari kuma tana da yara bakwai. A lokacin da na kai shekaru 6, na fara kula da kaina saboda bana samun kular. Daya daga cikin ‘yan uwana ke kaini kasuwa in yi bara amma kudin muna kaiwa mahaifiyarmu ce wacce take kula damu.

  “A lokacin da na kai shekaru 15, na yanke shawarar dawowa jihar Legas. Bayan isowata ne na hadu da mabarata hausawa da ke Agege kuma tare muke fita bara. Amma akwai wanda ke bamu wajen kwana, wanda shi ke kwace duk kudin da muka samu sannan ya bamu na abinci kawai. “

  Bayan shekaru uku da na dauka tare da shi, na koma Ajegunle inda na hadu da wani dan garinmu. Shi yake turani amma ina bashi wani kashi na kudin da muka samu. Daga nan ne na fara tara kudina har na siya mota kirar bas wacce na bada ana min haya. “Daga nan na kara siyan wata motar wanda daga haka ne na fara kasuwancin sufuri. Ina da motoci sama da 20 wadanda ke yawo daga Legas, Kano, Abuja, Kaduna, Jos da sauran jihohin arewa.” 

  Dikko ya bayyana cewa daga nan ne ya tafi gida Kano inda ya gina gida kuma ya zuba ‘yan haya a ciki. Amma kuma bai dena bara ba don ganin hakan yake kamar kasuwanci.Daga nan ya kara gina wasu gidajen hudu inda ya bada hayar biyu tare da saka matansa hudu da yaransa 18 a ciki. Kamar yadda yace, ya yi aikin haji har sau uku kuma yana kula da iyalansa yadda ya dace. “A shekaru biyar da suka gabata ne aka nada ni sarkin marokan Ajegunle kuma ina lura da lamurran bara da sasanci a tsakanin mabaratan. Amma ni yanzu na daina bara.” ya ce.

  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Sarkin maroka: Mabaracin da ya mallaki gidaje biyar, motoci 20 da kamfanin ruwan leda Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI