\ Rashin jituwa: Miji ya nike matar shi da mota a Saudiyya - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Rashin jituwa: Miji ya nike matar shi da mota a Saudiyya - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: bzglobalservicelabari@gmail.com "Colour" <#20124d>
 • LABARAN YAU

  Saturday, March 7, 2020

  Rashin jituwa: Miji ya nike matar shi da mota a Saudiyya

  - Fada tsakanin ma’aurata dai ya zama ruwan dare a kowanne yanki na duniyar nan - Akwai labaran fada tsakanin shugabannin kasashe da matansu, sarakuna da matansu, talakawa da matansu 

  - Wani magidanci ne yayi amfani da motar shi wajen banke matar shi a kan titi bayan sun samu sabani Fada tsakanin ma’aurata dai ya zama ruwan dare a kowanne yanki na duniyar nan. Dukkan ma’aurata na da banbanci da kuma kamanceceniya a wasu bangarorin rayuwa. Akwai labaran fada tsakanin shugabannin kasashe da matansu, sarakuna da matansu, 

  talakawa da matansu da sauransu. Babu inda aka isa a hana ma’aurata fada da juna, amma idan an tashi yi, ana yin ba hankali da kuma wanda ba za a yi dana-sani ba. Wani lamari ne ya faru a watan da ya gabata wanda ya tada hankulan jama’a masu tarin yawa. Ma’aurata ne suke fada a titi amma sai mijin yayi tsananin fushi. Tuni ya shiga motar shi sannan ya tuka tare da banke matar shi din. A nan kuwa ta fadai warwas ba a cikin hayyacinta ba. Wannan mummunan lamarin ya faru ne a titin birnin Khamis Mushait. Na’urar nadar al’amuran jama’a ce ta dauka sannan ya zagaye yanar gizo.

  Rashin jituwa: Miji ya nike matar shi da mota a Saudiyya Source: Twitter 

  A cikin bidiyon, an ga mijin na jiran matarshi a yayin da ya nuna zakuwar son yi mata magana. Amma kuma daga baya kawai sai ya shiga motar shi tare da tuka ta inda ya bige matar shi din. Daga baya kuma sai ga mijin na kallon matar tashi kwance a kan titi ba tare da ta san halin da take ciki ba. Majiya masu yawa sun tabbatar da cewa matar ta samu munanan raunika kuma an kwantar da ita a asbiti. Amma kuma ‘yan sanda sun damke mijin mara iya tankwasa zuciyar shi. Muna fatan wannan zai zama izinah ga ma’aurata ta yadda zasu kiyaye cutar da juna bayan anyi fada. LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Rashin jituwa: Miji ya nike matar shi da mota a Saudiyya Rating: 5 Reviewed By: Admin